An gano gawar da ta shafe shekara 800 hannayenta na rufe da fuskarta
Ana hasashen gawar ta shafe shekara 800 zuwa 1,200 a daure.
Wasu masu bincike daga Jami’ar San Marcos a Kasar Peru, sun gano wata gawa mai kimanin shekara 25 zuwa 30 daure da igiya, yayin da ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta.
An gano gawar ne da wadda aka kiyasta shekarunta tsakanin 800 zuwa 1,200 a garin Lima da ke kasar Peru, a ranar Talata, 30 ga watan Nuwamba 2021.
- ISWAP ta sace matafiya 15 a sabon a hari a Borno
- Bayan rikicin wata 9, jiragen Emirates za su ci gaba da aiki a Najeriya
Abun al’ajabin shi ne gawar ta shafe tsawon wannan shekaru fuskarta a rufe ba tare da hannayen sun bar kan fuskar ba.
Wani masanin ilmin kimiya na kayan tarihi, ya ce gawar ta fito ne daga yankin Lima na kasar.
Pieter Van Dalen Luna, na Jami’ar San Marcos, ya bayyana cewa “An daure jikin gawar duka da igiya kuma hannayenta sun rufe fuska,” inji shi.
Ya kara da cewa tsarin ya yi daidai da yadda al’ummar yankin ke binne gawa a wancan lokaci.
Van Dalen Luna, ya kuma ce mutumin ya rayu a cikin tsaunukan Andes, sai dai ya ce ba su da masaniyar jikin namiji ne ko na mace ne.
Masanin, ya ce gawar ta shafe tsawon wadannan shekaru ba tare da kashin gawar ko igiyar da aka daureta ya lalace ba.
Peru kasa ce wadda da ta yi fice wajen abubuwan da suka shafi tarihi, sama da shekaru 500.