An gano gawar mai kiwon macizai 124 a gidansa

Bincike ya nuna saran Maciji ne ta kashe mutumin

An gano gawar mai kiwon macizai 124 a gidansa

An gano gawar wani Ba’amurike da ke kula da macizai 124 a gidansa, inda aka tabbatar ya rasu ne sakamakon saran maciji, kamar yadda bincike ya nuna.

Mutumin, mai suna David Riston, mai kimanin shekara 49 na zaune ne a Jihar Maryland da ke Amurkan.

An gano gawar ce a gidansa tare da matattun macizai sama da 100 da ake zargin daya daga cikin majizan ne ya sare su bisa kuskure, kamar yadda wani bincike ya nuna.

Rasuwar tasa wani tsautsayi ne, kamar yadda jami’ai suka tabbatar.

Hukumomi sun yi watsi da cewa, xaya daga cikin macizai 124 ne ya kashe shi.

Wasu daga cikin macizan da aka samu a cikin kejin da aka tsare su a cikin gidansa, na da ban-mamaki kuma ba bisa ka’ida ake kula da su ba.

“Babu wanda ya san cewa yana ajiye macizai a cikin gidan,” inji Kakakin Gundumar Charles, Jennifer Harris.

Jennifer ta ce, macizan sun hada da jinsin gamsheka (cobras) da wasu bakaken macizai ‘black mambas’ da kuma mesa mai tsawon kafa 14.

Ana zargin daya daga cikin macizan da kashe David.

Kwararrun masanan dabbobi, sun cire dukkan macizan kwana guda bayan rasuwar David.

Mai magana da yawun ofishin Shugaban Gundumar Charles, Dianne Richardson ya ce an gudanar da bincike kan gawar David a Baltimore a ofishin kiwon lafiya na jihar.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Lafiya ta Jihar, Andy Owen, ya bayyana a cikin sakon imel cewa, bincike ya tabbatar da rasuwar David Riston, inda aka gano cewa dafin maciji ne ya yi ajalinsa.