An gano gawarwaki 5 a hatsarin kwalekwale mai mutum 100 a Naje
Kwalekwale dauke da fasinjoji akalla 100 ya yi hatsari a Karamar Hukumar Borgu ta Jihar Neja
Masu aikin ceto sun gano gawarkin mutum biyar bayan hatsarin kwalekwale mai dauke da sama da mutum 100 a Jihar Neja.
A halin yanzu ana ci gaba da neman sauran wadanda ba a gani ba bayan aukuwar lamarin a ranar Litinin a Karamar Hukumar Borgu.
Jami’in kula da bala’o’i na karamar hukumar, Musa Sa’id, ya sanar da haka, amma shugaban hukumar agajin gaggawa ta Jihar Neja, Abdullahi Baba Arah, ya ce ba a tantance hakikanin adadin wadanda suka rasu ko suka tsira ba.
A cewarsa, hatsarin ya ritsa da wani kwalekwale mai dauke da fasinjoji sama da 100 da kayan hatsi da sauransu da suka taso daga kauyen Dugga Mashaya na karamar hukumar za su je kasuwar Wara da ke Jihar Kebbi.
Jami’ain ya alakanta hatsarin da juyawar igiyar ruwa da kuma daukar kaya fiye da kima.
Jihar Neja dai ta sha fama da hadduran kwalekwale a ’yan watannin nan, lamarin da ya yi sanadin asarar rayuka da dama.
Kafin aukuwar wannan, na karshe shi ne wanda aka yi a Karamar Hukumar Shiroro, inda mutum akalla 10 suka rasu a watan Nuwamban 2023.
Gwamnan jihar, Umaru Bago ya yi ta’aziyyar wadanda suka rasu, tare da nuna damuwarsa game da yawaitar hatsarin kwalekwale a jihar.
Gwamnan ya umarci hukumomin da suka dace da su dauki matakan da suka dace, yana mai yabawa bisa saurin fara aikin ceto da masu ruwa da tsaki suka kaddamar bayan aukuwar lamarin.