An Gano Gurnetin ’Yan ta’adda 6 A Maiduguri

An gano gurneti guda shida da ake zargin ’yan ta’adda sun yi watsi da su a unguwar Ajilari Kross a birnin Maiduguri.

An Gano Gurnetin ’Yan ta’adda 6 A Maiduguri

Rundunar ’yan sandan jihar Borno sun gano wasu gurneti guda shida da ake zargin ’yan ta’adda sun yi watsi da su a unguwar Ajilari Kross a birnin Maiduguri.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Yusuf Lawal, ya ce an gano makaman ne a ranar Juma’a inda jami’an rundunar kula da na’urarori masu  fashewa (EOD), suka tantance gurnetin.

Ya ce tunin an yi binciken kwakwaf sosai kan yankin da abin ya shafa, kuma an tabbatar da babu aauran wata barazana a wajen.

Lawal ya bayyana cewa wani tashin hankali ya sake afkuwa a wannan rana a kauyen Bassam Galomari dake unguwar Gubio II a karamar hukumar Gubio.

Lawal ya ce jami’an tsaro sun ci gaba da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana, domin tabbatar da tsaron lafiyar jama’a da kuma kare cigaba da  afkuwar lamarin.

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar BRICS

Tags