An gano halittar da ta shekara miliyan 66 a cikin kwai tana jiran kyankyasa

Masana sun ce akwai yiwuwar halittar ta kai shekara miliyan 66 zuwa 72.

An gano halittar da ta shekara miliyan 66 a cikin kwai tana jiran kyankyasa

Halittar da aka gano mai shekara miliyan 66 Hoto: AFP

Masana ilimin kimiyya sun sanar da gano wata halitta da ta shafe kimanin shekara miliyan 66 a cikin kwanta, tana jiran kyankyasa ba tare da wani abu ya sameta ba.

An dai gano halittar da aka yi wa lakabi da ‘Yingliang’ ne a birnin Guangzhou da ke Kudancin kasar China, kuma an yi ittikfakin ta wata halitta ce da ake kira ‘Dinosaur’, wacce aka gano a cikin kwan nata.

“Tana daya daga cikin kwan Dinosaur mafi kyau da aka taba ganowa a tarihi,” inji Fion Waisum Ma, masani a Jami’ar Birmingham, wanda ya wallafa wata makala a mujallar iScience, kamar yadda ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP ranar Talata.

Fion dai tare da abokan bincikensa sun gano cewa an gano halittar ne kanta makale ne a kasan jikinta, yayin da kafofinta guda biyu suka kasance a tankwase.

Yanayin dai a cewarsu a bayan ba a cika ganinsa tare da halittar ba, sai dai a irin tsuntsaye na yanzu.

Halittun dai sun taba yin rayuwa ne a yankin da a yanzu ke zama nahiyar Asia ne da kuma Arewacin Amurka, miliyoyin shekaru da suka shude.

Halittar da aka gano din dai na da tsawon santimita 27 daga kanta zuwa bindi, kuma tana cikin kwan da girmansa ya kai kimanin santimita 17 ne a wani gidan tarihi da ke yankin na kasar China.

Masana dai sun yi ittifakin halittar za ta kai tsakanin shekara miliyan 66 zuwa 72, kuma ana kyautata zaton laka ce ta binne kwan, lamarin day a kare shi daga masu hake-hake.

Halittar dai tana daya daga cikin wadanda aka mance da su tsawon shekaru.