An Gano Haramtattun Matatu Da Litar Ɗanyen Mai 500,000 A Ribas
Mun gano haramtattun matatun mai akalla 10 da ke dauke da kimanin danyen mai lita dubu dari biyar.
Runduna ta musamman a Hukumar Sibil Difens ta bayyana cewa ta bankado wata haramtacciyar matata makare da kimanin lita dubu dari biyar ta ɗanyen man fetur a garin Odagwa da ke Karamar Hukumar Etche a Jihar Ribas.
Kakakin rundunar a jihar Ribas, Sufirtanda Olufemi Ayodele ne ya bayyana hakan yayin gabatar da waɗanda ake zargin ga manema labarai a Fatakwal, babban birnin jihar.
Olufemi ya bayyana cewa sun gano haramtattun matatun mai akalla 10 da ke dauke da kimanin danyen mai lita dubu dari biyar a waɗansu haramtattun ma’ajjiyu 50.
Ya kuma bayyana cewa sun samu wannan gagarumar nasarar ce ta hanyar amfani da kwarewa wurin tattara bayanan sirri da amfani da ƙwaƙwalwa wurin aiki.
Ya ce za su matsa kaimi wurin tabbatar da cewa sun hana satar ɗanyen man fetur da kuma hana ɗibar albarkatun ƙasa ba bisa ƙaida ba.
- Cibiyar Sarki Salman ta yi rabon tallafin abinci a Kano
- Za a saki mutum 200 da aka wanke daga zargin alaƙa da Boko Haram a Borno
“Baban kwamandan Sibil Difens, Dokta Ahmed Abubakar Audi ya lashi tokobin yaƙar masu yi wa tattalin arzikin ƙarsar nan zagon ƙasa.
“Ya kuma sha alwashin hukunta duk wanda aka kama da aikata irin wadannan ayyuka ko da kuwa wane ne ya tsaya musu.”
Kakakin rundunar ya ce tuni sun mika wadanda ake zargin ga rundunar ’yan sanda domin ci gaba da bincike da tabbatar da hukunci a kotu.