An gano jariri a bayan mahaifiyarsa awa 24 bayan ’yan bindiga sun kashe ta

Sai da ya kwana ya yini da kashe mahaifiyarsa, amma shi yana barci

An gano jariri a bayan mahaifiyarsa awa 24 bayan ’yan bindiga sun kashe ta

Jaririya

An gano wani jariri a goye a bayan mahaifiyarsa da ransa bayan kusan kwana biyu da yan bindiga suka kashe mahaifiyarsa a daji.

Bayanai sun nuna ’yan bindigar sun kashe mahaifiyar jaririn ne, amma yana goye a bayanta, haka ya kwana a dajin, har sai lokacin da aka je neman gawarwakin da aka kashe, inda aka tarar da shi a raye, yana kuma sharar barcinsa.

Lamarin dai ya faru ne a kan hanyar Pandogari zuwa Allawa da ke Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

Rahotanni sun nuna cewa ’yan bindigan sun tare motar da jaririn yake ciki ne da mahaifiyarsa a inda suka bude musu wuta suka kuma hallaka su,

A lokacin da ’yan bindagan suka yi musu harbin kan-mai uwa da wabi suka kashe su, shi yaron na kwance a bayan gawar mahaifiyar tasa yana barci, har lokacin da ’yan sa-kai suka je kan gawarwakin kashegari a dajin.

A zantawarsa da Aminiya, Shugaban Kungiyar Matasan Lakpama, yankin da abin ya faru, ya ce yaron da ke goye na daga cikin wadanda Allah Ya tsallakar a harin ’yan ta’ddan, sai kuma wani matashi.

“Abin da ban mamaki yaron na cikin wadanda Allah Ya yi suna da sauran shan ruwa a gaba a yayin da ’yan bijilan suka je wurin da abin ya faru domin kwashe gawarwakin kashegarin da abin ya faru, sai suka taras da yaron na goye na barci a bayan mahaifiyarsa, wacce aka dade da harbewa,” in ji shi.