An gano jaririya da ranta a cikin wani kabari

Yan sanda sun ceto wata jaririya da ake zargin an binne ta da ranta a Jihar Uttar da ke Arewacin Indiya. Wani mutum ne ya gano jaririyar a cikin wata tukunyar kasa a wani kabari lokacin da ya je binne ’yarsa da ta mutu dan lokaci bayan haihuwarta. Mutumin ya jawo hankalin ’yan sanda sannan […]

An gano jaririya da ranta a cikin wani kabari

Jaririn da aka binne

Yan sanda sun ceto wata jaririya da ake zargin an binne ta da ranta a Jihar Uttar da ke Arewacin Indiya.

Wani mutum ne ya gano jaririyar a cikin wata tukunyar kasa a wani kabari lokacin da ya je binne ’yarsa da ta mutu dan lokaci bayan haihuwarta.

Mutumin ya jawo hankalin ’yan sanda sannan aka kai jaririyar asibiti a yankin Bareilly kuma an ce tana samun lafiya.

’Yan sandan sun ce suna neman iyayenta da kuma wanda ya binne ta.

Shugaban ’Yan sandan Abhinandan Singh ya ce, ’yar mutumin da ya gano jaririyar ta rasu ne lokaci kadan bayan an haife ta bakwaini ranar Alhamis din makon jiya. Mutumin, wanda dan kasuwa ne ya je binne ’yarsa ne da yamma, sai ya iske jaririyar.

“A lokacin da suke haka kabarinta, sun kai kusan kamu uku, sai cebir ya doki tukunyar kasa wacce aka ciro. Sai aka ga jaririya a kwance a ciki’ ’Yan sanda sun dauki jaririyar zuwa asibiti inda take samun kula. Muna kokarin gano iyayenta kuma muna zargin cewa suna da masaniyar abin da ya faru da ita,” inji ta.

Bambancin jinsi a Indiya na daya daga cikin mafi muni a duniya. Ana yawan nuna wa mata bambanci kuma ana ganin ’ya’ya mata a matsayin wani nauyi musamman a al’ummomin da ke fama da talauci.

Masu fafutuka na ganin cewa fifita ’ya’ya maza da ake yi na nufin ana rasa miliyoyin ’ya’ya mata ga kisan ’ya’ya matan a shekarun da suka gabata.

Duk da cewa ana zubar da cikin ’ya’ya matan da ba a so da taimakon asibitocin da ke zubar da ciki ba bisa ka’ida ba, ba a saba ganin kisan jarirai mata bayan an haife su a kasar ba.