An gano jirgin kasan da ya bace shekara takwas a Masar

Hukumar Jirgin kasa ta kasar Masar ta gano wani jirgin kasan da ya bace kimanin shekaru takwas, inda aka ga alamunsa a Yammacin saharar kasar, kamar yadda jaridar kasar ta ruwaito. Jaridar Al Masry Al Youm ta bayyana cewa, an daina ganin jirgin ne lokacin da ya fice daga garin Dakhala da ke gundumar Yammacin […]

An gano jirgin kasan da ya bace shekara takwas a Masar
An gano jirgin kasan da ya bace shekara takwas a Masar

Hukumar Jirgin kasa ta kasar Masar ta gano wani jirgin kasan da ya bace kimanin shekaru takwas, inda aka ga alamunsa a Yammacin saharar kasar, kamar yadda jaridar kasar ta ruwaito.

Jaridar Al Masry Al Youm ta bayyana cewa, an daina ganin jirgin ne lokacin da ya fice daga garin Dakhala da ke gundumar Yammacin tsaunukan gabar ruwan Masar, tun a shekarar 2006. Bincike dai ya nuna barayi ne suka sace shi, inda suka kautar da shi daga kan tarragonsa da nisan kilomita 150, don haka jirgin ya kasa komowa,kamar yadda rahotanni suka bayyana. Sai dai ba a bayyana inda matukin jirgin yake ba.
Hukumar jiragen kasan kasar ta kafa kwamitin musamman da zai tsara yadda za a dawo da wannan jirgi kirar Jamus na Henschel a kan taragonsa. A ruwayar jaridar, kwmaitin ya gayyacin manyankamfanonin safara da su nemi aikin gyaran taragan jirgin sannan su mayar da su ga hukumomin kasar.
An dai kimanta kudin gyaran taragan da kimanin kudin Masar Fam miliyan biyu. Sannan ana sa ran ya ci gaba da aiki nan da shekara mai zuwa.
kasar Masar na daga cikin kasashen duniya da ke da jiragen kasa masu tsohon tarihi, amma tsarin safarar ya lalace a tsawon shekaru saboda yawan hudurra.