An gano kabari mai mutum 8,000 da dakarun Hitler suka kashe a Poland
An gano wani katon kabari da aka binne gawarwaki 8,000 da sojojin Nazi na tsohon Shugaba Jamus, Adolf Hitler, suka yi wa kisan kiyashi a lokacin Yakin Duniya na Biyu a kasar Poland. Wata Cibiya Mai Kula Muhimman Abubuwan a Kasar ta Poland ce ta ce ta gano kabarin. An dai gano shi ne a […]
An gano wani katon kabari da aka binne gawarwaki 8,000 da sojojin Nazi na tsohon Shugaba Jamus, Adolf Hitler, suka yi wa kisan kiyashi a lokacin Yakin Duniya na Biyu a kasar Poland.
Wata Cibiya Mai Kula Muhimman Abubuwan a Kasar ta Poland ce ta ce ta gano kabarin.
An dai gano shi ne a dajin Bialucki da ke kusa da Ilowo a kasar ta Poland a ranar Laraba, 13 ga watan Yulin 2022.
Cibiyar, wacce take binciken laifukan da aka aikata a lokacin yakin, da kuma a zamanin mulkin Kaminisanci, ta ce ta gano kabarin ne daga wani tarin toka mai yawan tan 15.8 na gawawakin da aka kone.
Kazalika, cibiyar ta kiyasta yawan tokar da gawarwakin, a inda ta fitar da yawansu ya kai kimanin na mutane akalla 8,000 ne.
Cibiyar ta kara da cewa, “Wannan shi ya ke nuna irin kokarin da Jamusawa suka yi na batar da sawun irin laifukan yakin da suka aikata na kisan kiyashi, ta hanyar kone gawarwaki a mamayar da suka yi wa gabashin Turai.”
A cewar Tomasz Jankowski, wanda ya jagoranci binciken da aka gano kabarin, “Kisan kiyashin da aka yi wa mutanen ya afku ne a wajen shekarar 1939, kuma yawancin wadanda aka kashe manya ne a kabilar Polish.”
A shekarar 1944, hukumomin Nazi sun tilasta wa fursunonin Yahudawa hako gawarwakin da sojojin Hitler suka yi wa kisan kiyashi, sannan su kone su.
Ta haka za su batar da duk wata shaidar laifukan yakin suka aikata, inji cibiyar.