An gano kabilar da mata da maza ke amfani da yaruka mabambanta a Jihar Kuros Riba

A Jihar Kuros Riba, an gano wata kabila mai suna “Obang” da ke magana da harshe biyu, tsakanisu wani ba ya fahimtar wani. Sun hadu ne a kan wani harshe daya da ake magana da shi na yankin sannan suke fahimtar juna, wadannan kabilu masu suna Okiro, Ofambe da kuma Okwereseng na yankin karamar Hukumar […]

An gano kabilar da mata da maza ke amfani da yaruka mabambanta a Jihar Kuros Riba
An gano kabilar da mata da maza ke amfani da yaruka mabambanta a Jihar Kuros Riba

Gwamnan Jihar Kuros Riba, Liyel ImokeA Jihar Kuros Riba, an gano wata kabila mai suna “Obang” da ke magana da harshe biyu, tsakanisu wani ba ya fahimtar wani. Sun hadu ne a kan wani harshe daya da ake magana da shi na yankin sannan suke fahimtar juna, wadannan kabilu masu suna Okiro, Ofambe da kuma Okwereseng na yankin karamar Hukumar Obudu ne kuma sun shafe sama da shekara dari zaune a wannan yanki.
Su dai wadannan al’umma, maza ba su fahimtar harshen mata, yayin da komai nasu aka hadu a jimlar wani yare daya da suke magana; kamar yadda a Arewacin Najeriya harshen Hausa ya zama harshen da kowace kabila kan yi magana da shi.
Aminiya ta ziyarci iyalan Mista Bonuface Nzama, dan kabilar Okiro, yayin da ita kuma matarsa ’yar kabilar Ofambe ce kuma tabbas yadda suka marabci wannnan jarida, wakilinmu ya nemi maigida Nzama da ya fassara abin da matarsa ta ce, sai ya yi murmushi ya ce: “Ai na riga na fada maka cewa ba ma jin yaren mata, su ma kuma haka ba su jin na maza.”
Haka kuma Uwargida Angela Nzama, da aka bukaci ta fassara abin da suke cewa a hirarsu da matan gidan sai ta ce: “Muna cewa ne maigida ya ce za a yi bako muna tattauna irin abincin alfarma, na fita kunyar bako da za mu yi masa ne, kwatsam sai muka ga kun shigo; shi ne muke cewa hala bakon namu ke nan. To ka ji abin da muke tattaunawa.”
Da aka bukaci Mista Bonuface Nzama ya yi karin haske game da lamarin yadda aka yi maza yarensu daban, mata ma haka sai ya ce: “Wannan lamari fa na da dadadden tarihi, domin iyaye da kakannin-kakanninmu sun yi iyakacin bakin kokarinsu su ga sun daidaita al’amarin amma ya ci tura sai dai kuma ana danganta hakan da tarihin da aka tsakuro daga cikin littafin Baibul; cewa an umarci wadannan kabilu ne uku da su gina gidan bauta gini mai tsawo kamar bene. Suna cikin aiki sai suka rikito kuma harsuna biyu suka rage da ake magana da su na want ton yanki. Shi ne sai aka raba wa maza nasu, mata ma haka. Haka dai muka samu tarihi.”
Aminiya ta bukaci jin irin yadda mai karatun wannan jarida zai iya gaskata hakan, cewa maza harshen da suke magana da shi ya bambanta da na mata. Sai shi da matarsa suka yi karin haske kamar haka: “Maza, muna kiran kofi da suna ‘Nkor’ yayin da su kuma mata suke kiransa da suna ‘Ugbala.’ Maza dai kan kira doya da suna ‘Kitong’ su kuma mata suna kiran doya da suna ‘Irue.”
Wannan ta sanya Aminiya ta tuntubi masana kan harsuna da al’adu, Farfesa Salisu Ahmad Yakasai. An tambaye shi game da lamarin sai ya ce: “Da farko zai iya faruwa, tun da daban-daban suke. Zai iya kasancewa mutum ya bar kabilarsa ko al’ummarsa ya tafi wata ya yi aure. Idan aka samu irin wannan wake da shinkafa, za ka iya ganin cewa kowa yana magana ne da yaren da ya fi fahimta.”
Wadannan kabilu dai an san da su, musamman mazauna jihar.