An gano kalanda mafi tsufa a duniya

Masu binciken dadaddun abubuwa na duniya, sun tono kalanda mafi dadewa a Aberdeenshire da ke Scotland, inda suka tono wata taska mai dauke da allo mai kwarmi 12, wadanda ke kwaikwayon siffar wata, da tafiyar watanni a kan rana.Gungun masanan da suka fito daga jami’ar Birmingham, sun yi nuni da cewa wannan kalandar mafarauta ne […]

An gano kalanda mafi tsufa a duniya

Kalanda mafi tsufa a duniyaMasu binciken dadaddun abubuwa na duniya, sun tono kalanda mafi dadewa a Aberdeenshire da ke Scotland, inda suka tono wata taska mai dauke da allo mai kwarmi 12, wadanda ke kwaikwayon siffar wata, da tafiyar watanni a kan rana.
Gungun masanan da suka fito daga jami’ar Birmingham, sun yi nuni da cewa wannan kalandar mafarauta ne da masu neman abinci a dajim, suka yi ta fiye da shekara dubu 10.
An fara tonon wannan taskar ne, da ke Warren Field, a shekarar 2004.
kwararrubn masanan sun yi nazarin ramuka, wadanda suka ce akwai yiwuwar suna da turakun katako. A cewar masaknan wannan tsohuwar kalanda ce, wadda aka yita a yankin Gabas ta tsakiya, kuma ta girmi kowa ce kalanda da dubban shekaru.n Wannan kalanda ta yi nuni da barazara da rani da damina da kaka.
bince Gaffney, Farfesa ne a fannin nazarin dadaddun abubuwa da ke Birmingham, wanda ya jagoranci masanan, ya ce: “Alamu  na nuni da cewa mafarautan Scotland na da suna da matukar kwarewa a tsawon shekaru, don hka suka rika bibiyar yanayim shekara. Kuma wannan ala’amari ya auku ne a tsawon shekara dubu biyar, tun kafin a samu irin kalandar da ake amfani da ita a Gabashi.
“Wannan aiki da aka yi, ya share fagen bincike wajen gano yadda aka tsara lissafin lokaci a cikin tarihi,” inji shi.

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu