An gano karin gawarwaki 13 na mutanen da hatsarin kwalekwalen Bagwai ya ci
Kawo yanzu mutum 42 suka rasu a hatsarin kwalekwalen da ya ritsa da daliban Islamiyya a harsu ta zuwa taron Mauludi
Yawan mutanen da suka rasu a hatsarin kwalekwalen da ya ritsa da matafiya a Karamar Hukumar Bagwai ta Jihar Kano ya karu zuwa 49.
Adadin ya kau ne bayan an gano karin gawarwaki 13 a hatsarin da ya ritsa da mutanen, cikinsu har da daliban Islamiyya da ke hanyarsu ta zuwa taron Mauludi.
- ASUU na shirin sake tsunduma yajin aiki
- Kotu ta sa ranar yanke hukunci kan ko Atiku ya cancanci tsayawa takara
Majiyoyi sun ce mutum 49 ne a kan kwalekwalen a lokacin da ya kife da fasinjojin, yawancin su daliban makarantar Madinatul Islamiyya da ke kauyen Badau a karamar hukumar.
Da farko bayan hatsarin, an ceto mutum bakawai daga cikin fasinjojin da ransu, aka kuma gano gawarwaki 29, kafin karin gawarwaki 13 da aka gano daga bisani.
Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano ya yi zargin cewa kayan da kwalekwalen ya dauka fiye da kima ne ya haddasa hatsarin, sannan ya kafa kwamitin bincike domin gano ainihin abin da ya faru.
Tuni dai gwamnatin jihar ta haramta amfani da kwalekwalen haya a yankin Bagwai, ta kuma bayar da bas-bas guda biyu domin a rika amfani da su wajen jigilar mutane tsakanin garin Bagwai da kauyen Badau.