An gano kudin Birtaniya mai shekara 435 a kasar Kanada
Wani mai zakule-zakulen tarkacen karafa a kasar Kanada, ya gano kudin Birtaniya da aka yi amfani da shi a karni na 16, makale a cikin tabon tsibirin bancouber. kwandalar da aka gano a yammacin Kanada, a kimanta shekarunta a matsayin shekara 435, don haka masana tarihin dadun al’amura sun yanke matsaya kan cewa wani mai […]
Wani mai zakule-zakulen tarkacen karafa a kasar Kanada, ya gano kudin Birtaniya da aka yi amfani da shi a karni na 16, makale a cikin tabon tsibirin bancouber. kwandalar da aka gano a yammacin Kanada, a kimanta shekarunta a matsayin shekara 435, don haka masana tarihin dadun al’amura sun yanke matsaya kan cewa wani mai yawo a kasashen duniya daga Birtaniya ne ya fara zuwa kasar Kanada, kafin matukan jirgin ruwan kasar Spain su gano kasar, karnoni da dama.
Dadaddun takardun tarihi na nuni da cewa kasar Spain ce kasa ta farko daga yankin Turai da ta fara shiga kasar Kanada, inda aka rika yi lakabi da Lardin British Columbia, a shekarar 1774, sai kuma shekara hudu baya rundunar sojojin gidan sarautar Birtaniya, suka shiga kasar a karkashin jagorancin Kyaftin James Cook.
Wani tsohon mai makala na’urorin tsaro, Bruce Campbell ne ya gano wannan kwandalar a watan Disambar bara tare da wasu sulallan Kanada masui dauke da shekarun 1891 da 1960 da kuma shekarar 1900.