An gano kushewar sarauniya a Masar bayan shekara dubu 4 da 500
Hukumomi a kasar Masar sun ce masu binciken kimiyyar kasar sun yi nasarar gano kushewar wata sarauniya a garin Abu-Sir da ke Kudu-maso-Yammacin birnin Alkahira, wadda ta rasu shekara 4,500 da suka wuce. Masanan sun gano kushewar ce a makabartar iyalan gidan Fir’auna Neferefre. Kuma sun yi amannar cewa kushewar ta mahaifiyarsa ce ko ta […]
Hukumomi a kasar Masar sun ce masu binciken kimiyyar kasar sun yi nasarar gano kushewar wata sarauniya a garin Abu-Sir da ke Kudu-maso-Yammacin birnin Alkahira, wadda ta rasu shekara 4,500 da suka wuce.
Masanan sun gano kushewar ce a makabartar iyalan gidan Fir’auna Neferefre. Kuma sun yi amannar cewa kushewar ta mahaifiyarsa ce ko ta mai dakinsa. Ministan da ke Kula da Kayayyakin Tarihin kasar Mamdouh el-Damaty ya bayyana sunan sarauniyar da Khentakawess, wanda aka rubuta a bangon kushewar. Kuma wannan ya sa ta zama Khentakawess ta III.
Amma jagoran masu binciken Miroslay Barta ya ce wurin da suka gano kabarin yana tabbatar masu da cewa na mai dakin fir’aunan ce. Har ila yau, ya ce an samu kayayyakin ayyukan gida akalla guda 30 a cikin kabarin. Jagoran ya kara da cewa wannan nasarar da aka samu za ta taimaka gaya wajen kara fahimtar tarihin gidan Sarautar kasar Masar na Biyar da na Shida, wadanda a zamaninsu aka gina Kabubburan Fir’aunoni kasar. Kuma garin Abu-Sir shi ne garin da tsohuwar masarautar kasar ta yi amfani da shi a matsayin makabartarta.