An gano likitan da yake zuba wa marasa lafiya maniyyinsa a mahaifa

Kowane dan Adam yana da asali, kuma da asalinsa za a iya bayyana shi, hakan ya sanya idan za a iya binciko asalin mutum ake duba mahaifiya ko mahaifinsa. Sai dai an samu akasin haka, bayan da aka samu wani likita da ake tuhuma cewa idan mata suka je asibitinsa sai ya yi amfani da […]

An gano likitan da yake zuba wa marasa lafiya maniyyinsa a mahaifa

Dokta Quincy Fortier

Kowane dan Adam yana da asali, kuma da asalinsa za a iya bayyana shi, hakan ya sanya idan za a iya binciko asalin mutum ake duba mahaifiya ko mahaifinsa.

Sai dai an samu akasin haka, bayan da aka samu wani likita da ake tuhuma cewa idan mata suka je asibitinsa sai ya yi amfani da maniyyinsa wajen yi musu ciki.

Maza da mata na tuntubar likitan wanda ke birnin Pioche a Jihar Nevada ta kasar Amurka.

Likitan mai suna Dokta Quincy Fortier, wani rahoto da aka fitar a ranar 2 ga Disamba da aka wallafa kansa ya nuna cewa, sama da shekara goma likitan ya dauka yana yi wa mata marasa lafiya ciki a wani asibitin mata da mallakinsa ne.

Abu muhimmi a nan shi ne yadda aka haifi wadansu ’ya’yan da maniyyinsa, kuma ba wanda ya gano cewa likitan ne mahaifinsu har sai da ta kai ga an yi gwajin kwayar halitta (DNA) sannan aka tabbatar da cewa, likitan ne mahaifin ’ya’yan da matan suka haifa bayan da suka ziyarci asitibitinsa.

An yi gwajin DNA a wasu wuraren kuma an samu sakamakon iri daya da ya tabbatar da kwayar halittar likitan ne.

Wata mata mai suna Hanna Olsons wadda ta bayyana takaicinta kan abin da likitan ya aikata, ta ce likitan bai yi haka don samun zuriya da matan da ya yi wa hakan ba, sai dai kawai don cin amana, alhali  wannan ba ya nufin Dokta Quincy Fortier na da wani tabin hankali da ya sanya shi ya rika amfani da maniyyinsa wajen yi wa marasa lafiya cikin.

A cikin wadanda Dokta Quincy Fortier ya yi wa ciki akwai ’yar dan uwansa da wadansu matan daban.

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou