An gano ma’adanin Nikel a Jihar Kaduna
Ma’aikatar Bunkasa Ma’adanai ta tabbatar da gano ma’adanin Nikel kauyen Dangoma da ke Jihar Kaduna, inda ta ce an gano ma’adanin a watannni da suka gabata, kuma kwararru daga ma’aikatar suna bin diddigin lamarin kamar yadda doka ta tanada.Wani kamfani mai zaman kansa na kasar Ostireliya a karkashin Mista Hugh Morgan da ya kware wajen […]
Ma’aikatar Bunkasa Ma’adanai ta tabbatar da gano ma’adanin Nikel kauyen Dangoma da ke Jihar Kaduna, inda ta ce an gano ma’adanin a watannni da suka gabata, kuma kwararru daga ma’aikatar suna bin diddigin lamarin kamar yadda doka ta tanada.
Wani kamfani mai zaman kansa na kasar Ostireliya a karkashin Mista Hugh Morgan da ya kware wajen gano ma’adanai a sassan duniya ne ya gano ma’adanin, inda ya ce yana da ga cikin mafiya inganci a duniya kamar yadda wata jaridar kasar mai suna The Australian ta ruwaito. A cewar jaridar gano ma’adanain abu ne da ya bayar da mamaki saboda an samu ma’adanin nikel ne a kananan kwallaye a tsawon milimita3 a karkashin kasa wanda hakan ke nuni da cewa za a samu babban dutsen ma’adanin a filin da aka gano din.
Shi dai ma’adanin nikel wani farin karfe ne mai shigen zinare da ake matukar bukatarsa a kasuwannin duniya kuma ana amfani da shi wajen kera tsabar kudade da sauran kayayyaki masu daraja inda ake sayar da labarsa daya a kan Dala hudu da Senti 43 (kimanin Naira 1,770).
Manyan kasashen da suke samar da shi a duniya sun hada da Ostireliya da Botswana da Brazil da Indonusiya da Kanada da China da Philippine da Kyuba da Kolombiya, kuma ana sa ran idan aka same shi da yawa yana iya kawo wa kasar nan kudin shiga fiye da man fetur a nan gaba.
“Ma’aikatar Bunkasa Ma’adanai tana sane da murnar da ake yi a kafafen watsa labarai dangane da gano ma’adanin nikel a wasu sassa na Jihar Kaduna. Hakika wannan abin jin dadi ne bisa lura da wani bangare na muhimmancin ma’adanin da ake magana. Kuma ma’aikatar tana sane da yawan gano ma’adanin a yankin. Tun gano ma’adanin watannin da suka gabata, kwararru daga ma’aikatar suke ta bin diddigin wannan batu kamar yadda doka ta tanada,” inji sanarwar ma’aikatar.
Ta kara da cewa: “Amma muna kira ga jama’a su kyale ma’aikatar ta fito da cikakken bayani kan abin da aka gano,” inji sanarwar dauke da sanya hannun Babban Sakataren Ma’aikatar Mohammed Abbas.
Ministan Bunkasa Albarkatun Ma’adanai Dokta Kayode Fayemi, ya sha nanata niyyar Najeriya ta bunkasa fannin ma’adanai ta hanyar zuba jarin biliyoyin Dala a fannin.
A farkon wannan wata ya shaida wa mujallar Bloomberg cewa za a zuba jarin Dala biliyan biyar don fara bunkasa sashin. “Kuma nan da shekara biyu zuwa biyar za mu fara sana’anta dangogin karafa da kwal da zinare masu dimbin yawa,” inji shi.