An gano maganin da zai iya warkar da Ebola
A shekaranjiya Laraba ne masana kimiyya a kakar Amurka sun ce wani maganin gwaji na kwayar cutar Ebola, ya ceci rayuwar wasu birrai uku da suka kamu da kwayar cutar kuma maganin zai iya aiki a kan dan Adam, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana. Masu binciken a jami’ar Tedas, sun ce […]
A shekaranjiya Laraba ne masana kimiyya a kakar Amurka sun ce wani maganin gwaji na kwayar cutar Ebola, ya ceci rayuwar wasu birrai uku da suka kamu da kwayar cutar kuma maganin zai iya aiki a kan dan Adam, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana.
Masu binciken a jami’ar Tedas, sun ce an sanya kwayar cutar ta Ebola a jikin birran, wadda ita ce sanadiyyar barkewar annobar cutar a yankin Yammacin Afirka bara.
Daga nan sai aka ba su magani, bayan kwana uku kuma suka rayu duk da tsananin zazzabi da yawan kwayar cutar a jikinsu.
Dokta Aledander ban Tullecan, kwararre a kan cutar ta Ebola, ya ce za a iya samar da maganin cikin makonni takwas kuma za a iya sarrafa shi domin maganin nau’in kwayar cutar daban-daban. ‘’Ina ganin abin sha’awa da wannan magani, shi ne za a iya amfani da shi a kan nau’in kwayar cutar ta Ebola daban-daban, saboda haka wannan gwajin, ba ya nuna cewa za mu iya amfani da maganin ko da kwayar cutar ta rikide ta sauya yanayi,’’ inji Doktan.
Cutar Ebola dai ta hallaka mutane da dama a yankin Afirka ta yamma musamman a kasashen Guinea da Laberiya da Saliyo.