An gano mai karbar albashin malamai 1,832 a Filato

Aikin tantace ma’aikatan Jihar Filato ya gano wani mutum da ke karbar albashin malaman makaranta dubu daya da 832 alhali shi ba malamin makaranta ba ne, yayin da dimbin masu cin gajiyar albashin ma’aikatan bogin suka gudu suka bar albashinsu a asusunan bankuna.Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Lalong ne ya bayyana haka, inda ya ce […]

An gano mai karbar albashin malamai 1,832 a Filato
An gano mai karbar albashin malamai 1,832 a Filato

Aikin tantace ma’aikatan Jihar Filato ya gano wani mutum da ke karbar albashin malaman makaranta dubu daya da 832 alhali shi ba malamin makaranta ba ne, yayin da dimbin masu cin gajiyar albashin ma’aikatan bogin suka gudu suka bar albashinsu a asusunan bankuna.
Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Lalong ne ya bayyana haka, inda ya ce mutumin wanda ya yi ikirarin karbar albashin malaman 1,832 da yake zaune a kasar Amurka shekara da shekaru da har yanzu ba a gano ko wane ne ba, ya shida masa ta wayar tarho cewa, yana karabar albashin ne domin amfanin kansa da kuma ma’aikatan bogi da dama domin ya samar da kudi ga ayyukan jinkai ga matan da mazansu suka mutu da kuma marayu.
Gwamna Lalong ya bayyana haka ne a ranar Asabar da ta gabata da daddare lokacin da yake ganawa da manema labarai a gidan gwamnati da ke Jos, domin bikin cikarsa shekara daya a kujerar mulki, inda ya ce gwamnatinsa ta gaji bashin albashi da ya kai Naira biliyan daya da miliyan 700, wanda ya ci gaba da gudana a haka na tsawon lokaci bayan bayanai sun nuna ma’aikata da dama kodai sun yi ritaya ko sun mutu. Ya yi bayaninh cewa dubban ma’aikatan bogi da ke cikin jerin albashin ma’aikatan gwamnati ne suke jawo aukuwar haka.
Gwamna Lalong ya ce “Rahoton farko na aikin tantace ma’aikatan ya nuna wani mutum guda wanda ba malamin makaranta ba ne, ya sanya jabun sunayen mutum 1,832 kuma ya bude asusun ajiyar banki da sunansu wadanda ta hanyarsu albashin malamai ke sulalewa duk wata kafin lambar asusun ajiyar banki na BbN ya fallasa shi.”