An gano mai karbar albashin mutum 200 a Jihar Sakkwato
Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya ce jihar na asarar kimanin Naira miliyan 300 a kowane wata wajen biyan albashi a kananan hukumomi jihar kafin gudanar da binciken kwakwaf don gano ma’aikatan bogi.Gwamna Aminu Tambuwal ya bayyana haka ne a ranar Litinin da ta gabata lokacin da yake zantawa da manema labarai kan […]
Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya ce jihar na asarar kimanin Naira miliyan 300 a kowane wata wajen biyan albashi a kananan hukumomi jihar kafin gudanar da binciken kwakwaf don gano ma’aikatan bogi.
Gwamna Aminu Tambuwal ya bayyana haka ne a ranar Litinin da ta gabata lokacin da yake zantawa da manema labarai kan cikarsa shekara daya da hawa karagar mulkin jihar.
Gwamna Tambuwal ya ce: “Binciken ma’aikatan bogi da muka yi ya nuna muna asarar Naira miliyan 300 a kowane wata a kananan hukumomi 23 da muke da su, akwai wata karamar hukuma da aka samu rarar Naira miliyan biyar ana neman masu albashin amma ba su zo ba. Kuma akwai wani mutum daga Jihar Zamfara da aka samu yana karbar albashin mutum 200 wadanda dukkansu ba ’yan asalin Jihar Sakkwato ba ne. Cuwa-cuwa ta yi yawa a kananan hukumomin, saboda haka muka ki rantsar da shugabannin kananan hukumomin har sai an kammala tantance ma’aikatan.”
Gwamna Tambuwal ya ce gwamnatinsa ta bayar da aikin ginin Asibitin Mutala da ke birnin Sakkwato kan Naira biliyan daya da miliyan 400, baya ga maganin da suka sayo domin a rika bai wa marasa lafiya mata da kananan yara kan Naira biliyan daya.
Gwamnan ya ce za su kafa hukumar kula da amfanin gona domin bunkasa aikin gona ta yadda duk wani manomin da ya noma albasa ko makamancinta gwamnati za ta saya ta san yadda za ta yi da ita. Kuma ya ce gwamnatinsa za ta yi iya kokarinta kawo shirye-shiryen da za su rage wa mutane radadin wahala a lokacin azumin bana.
Da ya juya kan maganar da take yawo cewa ya cika yawo ba ya zama a gari, sai Gwamna Tambuwal ya ce “Masu fadin cewa ni Gwamnan yawo ne su sani duk tafiyata kan aikin gwamnati ce, kuma zamani ya zo duk inda mai mulki yake yana iya jagorantar jiharsa kuma ina kalubalantar kowa ya gaya min inda aka samu cikas a aikin gwamnati don ba ni nan. Yawona bai hana ruwa gudu a cikin jagorancina ba, ba abubuwan shiga dole ne ka tashi ka nemo su a wurare daban-daban. Ni ma ina son in zauna in huta kamar kowa, na tashi tsaye ba ina yawon sharholiya ba ne.”