An gano makarantun firamare na bogi 12 a karamar Hukumar Zariya

A ci gaba da aikin tantance ma’aikata da Gwamnatin Jihar Kaduna take yi a kananan hukumomin jihar don gano jabun ma’aikata, Shugaban riko na karamar Hukumar Zariya Barista Jafaru Abbas ya ce an gano makarantun firamare na bogi guda 12 a yankinsa.Barista Jafaru Abbas ya bayyana haka ne a lokacin da yake mai da martani […]

An gano makarantun firamare na bogi 12 a karamar Hukumar Zariya
An gano makarantun firamare na bogi 12 a karamar Hukumar Zariya

A ci gaba da aikin tantance ma’aikata da Gwamnatin Jihar Kaduna take yi a kananan hukumomin jihar don gano jabun ma’aikata, Shugaban riko na karamar Hukumar Zariya Barista Jafaru Abbas ya ce an gano makarantun firamare na bogi guda 12 a yankinsa.
Barista Jafaru Abbas ya bayyana haka ne a lokacin da yake mai da martani kan zanga-zanga da garkuwa da shi da wasu daga cikin ma’aikatan karamar hukumar suka yi kan lamarin.
Shugaban ma’aikata na karamar hukumar Shehu Muhammed Tukur ya shaida wa Aminiya cewa tarzomar tare da garkuwa da shugaban karamar hukumar ta biyo bayan tantance ma’aikata da ake gudanarwa ne inda wadanda ba su ga sunansu ba suka gudanar da tarzomar.
Barista Jafaru ya ce tantance ma’aikatan ana yi ne domin a san adadin ma’aikatan da karamar hukumar ke da shi, kuma an samu nasara sosai a tantancewar da ake yi, “Wadanda suke yin boren sun karya ka’idar farko ta tantancewa da gwamnatin Jihar Kaduna ta gudanar, don haka sunayensu ba su fito a jerin sunayen da gwamnatin ta ba mu ba, don haka muka ce ba za su shiga cikin tantancewar ba, sai sun koma kwamitin farko da gwamnatin jiha ta kafa ya wanke su kafin su zo ga wannan kwamiti. Wannan dalilin ne ya sa suke bore tare da garkuwa da ni a ofis dina, kuma ina shaida maka yanzu haka mun gano makarantun firamare na karya guda 12 da babu su kwata-kwata amma ana karbar kudin gudanar da su, don haka wannan aiki da muke yi na tantance ma’aikata ba za mu fasa ba domin gyara muke nema,” inji Barista Jafaru.