An gano malaman makaranta 167 na bogi a Lere
Karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna ta gano malaman makarantar firamare na bogi guda 167, cikin sababbin malaman firamare guda 614 da aka dauka a kwanakin baya. Sakataren Karamar Hukumar kuma shugaban kwamitin binciken malaman makarantun da Karamar Hukamar ta kafa, Injiniya Ahmed Yahaya Lere ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa […]
Hussaini Isah, Jos
Karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna ta gano malaman makarantar firamare na bogi guda 167, cikin sababbin malaman firamare guda 614 da aka dauka a kwanakin baya.
Sakataren Karamar Hukumar kuma shugaban kwamitin binciken malaman makarantun da Karamar Hukamar ta kafa, Injiniya Ahmed Yahaya Lere ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Saminaka.
Ya ce sun gudanar da bincike tare da tantance sababbin malaman da aka dauka a wannan Karamar Hukuma guda 614 a kwanakin baya. Ya ce a binciken da suka yi, sun gano cewa a wannan Karamar Hukuma an debi sababbin malamai guda 614, kuma aka tura su makarantu daban-daban na yankin.
Ya ce bayan binciken wadannan sababbin malamai da aka dauka, ta hanyar gabatar da takardun daukarsu aiki, da takardun makarantun da suka gama. Sun gano cewa malamai guda 167 suna da matsalolin da suka hada da yadda wasu tun da aka dauke su ba su je wuraren da aka tura su ba. Wadansu tun da suka zo ba su fi kwana 1 ko 2 ba suka bace abinsu. Wadansu kuma ana ganin na bogi ne, an sa sunansu ne kawai a tsarin biyan albashi.
Har’ila yau ya ce “cikin wadannan malamai masu matsaloli kashi 90 ba ‘yan asalin Karamar Hukuma ba ne. Wasu daga Abuja da Kaduna da Kano da Ogun da Enugu da sauran wurere masu nisa suke.
Hukumar kula da makarantun firamare ce, ta dauki wadannan malamai, amma albashinsu daga karamar hukuma yake zuwa. Don haka muka shigo don ganin mun tantance tare da gano gaskiyar al’amari, don ganin ba mu rika biyan albashi ga mutanen da ba su da tabas cewa ma’aikata ne ba.”
“Shi ne sai muka ga cewa da mu yi ta biyan albashi a haka, bari mu tantance su domin mu gano gaskiyar al’amari. Kuma hanyar da aka dauki wadannan malamai, ita ce za mu bi mu sake daukar wasu malaman domin cike gurbin wadannan malamai na bogi, da muka samu,” Inji shi.
A karshe Sakataren ya yi kira ga dukkan wadanda suka cancanta da ke wannan yanki, su zo su nemi wannan aiki, domin a dauke su.