An gano maniyyata takwas masu juna biyu a Yobe
An gano wasu mata maniyyata su takwas dauke da juna biyu a Jihar Yobe da suka yi kunnen kashi ga kiraye-kirayen da Hukumar Alhazan Jihar ke yi na matan da ke da juna biyu, su hakura da zuwa Saudiyya don sauke farali har sai sun haihu, lokacin da na’urar tantancewa ta fallasa su.Sakataren Hukumar Alhazai […]
An gano wasu mata maniyyata su takwas dauke da juna biyu a Jihar Yobe da suka yi kunnen kashi ga kiraye-kirayen da Hukumar Alhazan Jihar ke yi na matan da ke da juna biyu, su hakura da zuwa Saudiyya don sauke farali har sai sun haihu, lokacin da na’urar tantancewa ta fallasa su.
Sakataren Hukumar Alhazai ta Jihar Yobe, Alhaji Bukar Kime ya shaida wa Aminiya haka a Damaturu, inda ya ce hukumarsu ta jajirce tare daukar matakin ba sani ba sabo a aikin tantance mata masu juna biyu, inda ya ce hakan ne ya ba su damar zakulo masu juna biyu tare da maye gurabensu da wasu.
Ya shawarci mata masu juna biyun su hakura zuwa shekara mai zuwa ko kuma suna da zabin a mayar musu da kudinsu.
Alhaji Bukar Kime ya kara da cewa, bayan wadannan mata masu juna biyu da aka gano a yayin tantance maniyyatan har wayau sun kuma gano wadansu mutum uku da a bara hukumomin Saudiyya suka dawo da su kasar nan saboda watakila laifuffukan da suka aikata, amma sai ga shi a bana ma sun yi shigar burtu don sake komawa.
Daga nan sai ya shawarci dukkan maniyyatan jihar su guji saba wa dokokin kasar nan da kuma na kasar Saudiyya don kada su jawo wa kansu shiga halin tsaka mai wuya a yayin da suke aikin Hajjin.
Sakataren ya bayyana irin tallafin da gwamnatin Jihar Yobe ta yi ga maniyyatan jihar da suka hada da Riyal 300 ga kowane maniyyaci da tanadar musu da masauki kusa da Harami da tanadar musu da Ihrami kyauta da kuma samar musu da kwararrun likitoci da malaman da za su rika fadakar da su dokokin aikin Hajji da makamantansu.