An gano masana’antun jarirai a Akwa Ibom
Rundunar ‘Yan sandan jihar AkwaIbom ta gano wadansu‘yan mata guda bakwai masu tsohon ciki da aka boye su a wani gida ana jiran ranar da za su haihu domin a sayi abin da suka haifa, inda za a biya su makudan nairori.Kwamishinan’yan sandan jihar Umar Gwadabe ne ya sanar da manema labarai haka a uyo.Aminiya […]

Rundunar ‘Yan sandan jihar AkwaIbom ta gano wadansu‘yan mata guda bakwai masu tsohon ciki da aka boye su a wani gida ana jiran ranar da za su haihu domin a sayi abin da suka haifa, inda za a biya su makudan nairori.
Kwamishinan’yan sandan jihar Umar Gwadabe ne ya sanar da manema labarai haka a uyo.
Aminiya ta gano cewa an gano wadannan ‘yan mata a wani layi mai suna layin Nepa da ke garin IkotE kpenej a ihar Akwa Ibom bayan da aka kyankyasa wa rundunar ‘yan sanda.
Haka kuma an tabbatar wa Aminiya cewa wata daga cikin ‘yan matan ta haihu lokacin da ‘yan sanda suka je maboyar tasu, shi ne ma sanadin da ya sanya ‘yan sandan suka gane inda ake boye da ragowar mata masu cikin, wadanda shekarunsu ya kama daga goma sha biyar zuwa ashirin da biyar.
Idan za a iya tunawa dai, a makon da ya gabata ma an kama wata mata mai suna Maobongata da ita ma take dillancin jarirai a wannan jihar.
Aminiya ta tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom DSP Etim Dickson, game da lamarin inda ya ce “ka san a cikin kowace al’umma akwai nagari, an sanar mana cewa akwai wani mutum mai suna Emma Thompson wanda akalla zai kai shekara talatin da biyar da haihuwa da ya hada baki da wata mata mai lakabin “Mama Nas” suna gudanar da wani asibitin karya don cutar jama’a suna karbar haihuwa,idan an haifi jaririn sai su sayar, suna ajiye ‘yan mata domin gudanar da wannan kazamar harkar”. Inji shi
Wadansu daga ckin ‘yan matan, watau, Ikwo Johnson Ofuo da Joy Michael John, sun tabbatar wa ‘yan sandan yayin da aka bincike su cewa idan da namiji aka haifa ana sayarwa kan kudi Naira dubu 400, idan kuma ‘ya mace ce,ita kuma ana saye kan Naira dubu 350.”.
Haka kuma rundunar ‘yan sandan ta nuna wa manemal abarai wata mata mai suna Doreen Temple, daga kkuyen IduUruan, da ake tuhumarta da laifin satar dan dan uwanta mai suna Jesse Benson, domin kai shi kasar waje ya yi aikin barantaka, Da kuma wata unguwarzoma da ake zargi da karbar haihuwar irin wadancan jarirai ba bisa ka’ida ba.
Rundunar ‘yan sanda ta ce da zarar ta kammala bincike za a gurfanar da su a gaban kotu.