An gano masu yi wa kasa hidima a cikin kungiyar asiri a Anambra

Wadansu masu yi wa kasa hidima a Jihar Anambra, Rukunin A na 2019 sun bayyana ficewarsu daga cikin kungiyar asiri. Jami’i mai kula da masu yi wa kasa hidimar a jihar Mista Kehinde Aremu ne ya bayyana haka a wajen bikin kammala horon da ya gudana a dandalin masu yi wa kasa hidimar da ke […]

An gano masu yi wa kasa hidima a cikin kungiyar asiri a Anambra

Masu yi wa qasa hidima suna fareti

Wadansu masu yi wa kasa hidima a Jihar Anambra, Rukunin A na 2019 sun bayyana ficewarsu daga cikin kungiyar asiri. Jami’i mai kula da masu yi wa kasa hidimar a jihar Mista Kehinde Aremu ne ya bayyana haka a wajen bikin kammala horon da ya gudana a dandalin masu yi wa kasa hidimar da ke Umunya.

Ya ce, an samu rahoton wadansu daga cikin masu yi wa kasar hidima da suka tuba daga mummunar dabi’ar nan ta shan miyagun kwayoyi.

Hakazalika a cikin mako uku an samu masu yi wa kasa hidima da suke cikin  kungiyar asiri, sun bayyana ficewarsu daga kungiyar.

Kehinde, ya ce wadanda suka tuba za a mika su ga Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun Kwayoyi (NDLEA) domin kula da su.

Babban jami’in ya bukaci  masu yi wa kasa hidimar su kasance jakadu nagari, kuma su zama abin misali ga sauran matasa. Ya yi fatar ba za su koma cikin wannan mummunar dabi’a ba.

A cewar Mista Kehinde babban abin farin ciki ne yadda wadansu masu yi wa kasa hidima biyu suka yi musayar zoben aure a tsakaninsu, wanda hakan na nuni da irin manufofin jihar ta Anambra na hadin kan kasa.

A jawabin Gwamnan Jihar Anambra, Willie Obiano, ya ce gwamanatinsa za ta kara alawus din da take bai wa masu yi wa kasa hidima. Ya ce za a ba da dama, wajen ba da gudunmawarsu ta hanyar aiwatar da tsare-tsare musamman a fannin samar da ingantaccen ilimi da kiwon lafiya da aikin noma da sauransu. Kwamishinan Matasa da Bunkasa Tattalin Arziki, Mista Bonabenture Enemali, wanda ya wakilci Gwamnan a wajen bikin kammala horo na masu yi wa kasar hidima da aka yi mako uku ana yi.