An gano matattarar dillalan kwaya kusa da ofishin ’yan sandan Abuja
An bankado wata matattarar dillalan miyagun kwayoyi da ke kusa da wani ofishin ’yan sanda a Abuja.
An bankado wata matattarar dillalan miyagun kwayoyi a kusa da wani ofishin ’yan sanda a Birnin Tarayya, Abuja.
Jami’an Kwamitin Tababatar da Tsaftar Muhalli karkashin Hukumar Kula da Birnin Tarayya ne suka gano matattarar dillalan kwayar suka kuma tarwatsa ta.
- Yadda aka ceto mutum 113 daga gidan mari a Kano
- ‘Najeriya ce kasa ta 8 mafi hadari a duniya’
- Daga Laraba: Yadda labaran karya ke hana ruwa gudu a cikin al’umma
A lokacin da suka kai samamen, jami’an sun kama wasu mutum biyu da tabar wiwi mai nauyin kilogram 45 a wurin da ke mahadar hanyar Dutse zuwa Bwari.
Kamen dai ya sanya mutane mamaki inda suka yi ta tattaunawa a kai, ganin cewa ’yan taku ne tsakanin maboyar dillalan kwayar da wani ofishin ’yan sanada.
Babban Hadimi na Musamman Ministan Birnin Tarayya kan Sanya Ido da kuma Tabbatar da Bin Doka, Attah Ikharo, ya ce sun kai samamen lalata wurin ne bayan bayanan sirri da suka samu kan ayyukan dillalan miyagun kwayoyi.
A cewarsa, tabbatar da gaskiyar rahoton ke da wuya, Ministan Birnin Tarayya, Muhammad Bello, ya ba da umarnin a lalata wurin ba tare da bata lokaci ba.
Attah Ikharo ya bayyana takaicinsa game da halayyar wasu mazauna yankin da ke rufa wa masu sayar da miyagun kwayoyi asiri.
Ya bayyana cewa tuni hukumar Birnin Tarayya ta mika miyagun kwayoyin da aka kama ga Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna (NAFDAC) domin ta gudanar da bincike.