An gano mutumin da ya kai harin birnin Paris

Firayi Ministan Faransa Manuel balls ya ce ’yan sandan kasar sun gano mutum na uku cikin mutanen da suka kai hari a gidan rawa na Bataclan da ke birnin Paris a watan jiya.Mutum 90 ne dai aka kashe a harin da aka kai a gidan rawar.Mista balls bai bayyana sunan mutumin ba, sai dai bai […]

An gano mutumin da ya kai harin birnin Paris
An gano mutumin da ya kai harin birnin Paris

Firayi Ministan Faransa Manuel balls ya ce ’yan sandan kasar sun gano mutum na uku cikin mutanen da suka kai hari a gidan rawa na Bataclan da ke birnin Paris a watan jiya.
Mutum 90 ne dai aka kashe a harin da aka kai a gidan rawar.
Mista balls bai bayyana sunan mutumin ba, sai dai bai musanta rahotannin da ke cewa sunan mutumin Fouad Mohamed-Aggad daga Jihar Strasbourg ba, kamar yadda BBC ya bayyana.
Wata jaridar kasar, Le Parisien, wacce ta ambato wata “majiya mai tushe,” ta ce mutumin ya koma Faransa ne daga kasar Siriya.
Sauran mutum biyu da suka tayar da bama-baman da ke jikinsu a gidan rawar su ne Omar Ismail Mostefai, dan shekara 29 da Samy Amimour, dan shekara 28, kuma dukkansu ’yan kasar Faransa ne.