An gano sabon irin masara mai jure fari da ƙwari

Cibiyar Bincike Aikin Noma (IAR) ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a wani sabon bincike da ta gudanar ta gano tare da samar da wani sabon irin shuka na masara da ke bijire wa wasu nau’o’in cututtukan tare da jure wa matsakaicin fari. Shugaban Cibiyar Farfesa Muhammad Faguji Isiaku ne ya bayyana haka, a […]

An gano sabon irin masara mai jure fari da ƙwari

Gonar Masara

Cibiyar Bincike Aikin Noma (IAR) ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a wani sabon bincike da ta gudanar ta gano tare da samar da wani sabon irin shuka na masara da ke bijire wa wasu nau’o’in cututtukan tare da jure wa matsakaicin fari.

Shugaban Cibiyar Farfesa Muhammad Faguji Isiaku ne ya bayyana haka, a jawabinsa a yayin bikin kaddamar da gabatar da sabon irin shukar ga manoma a wani buki da aka yi wa lakabi da ‘Gani ya kori ji’ wanda aka gudanar a ƙauyen Kakkangi da ke karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.

Sabon irin shukar da aka yi wa lakabi da ‘Tela’ mai juriya ga kwari zai sa gwamnati ta samu rarar kudi na biliyoyin Naira da take amfani da su wajen sayen maganin feshin kwari daga kasashen waje, wanda rashin maganin ke haifar da koma baya a kokarinta da na  manoma na samar da wadataccen abinci a kasa.

Shugaban Cibiyar ya jinjina wa manoman da suka rungumi sabbin fasahohi da kuma dabarun noma da cibiyar ta bullo da su a inda suke jarraba su domin ci-gaba.

“Kokarin da kuke yi ne na karbar irin wadannan fasahohi da dabarun noma gaba-gadi daga gare mu ya sa wannan cibiya ta samu karfin gwiwar gabatar muku da wannan sabuwar fasaha na irin shuka kai-tsaye ba tare da wani gwaji ba.

“Gaskiya karbar sabon abu musamman ma irin wannan da kuma amfani da shi kai tsaye ba tare da fargabar abin da ka iya biyo baya ba, ba karamin abu ba ne.

“Sai dai na yi amanna da cewa yanzu manoma na matukar farin cikin ganin amfanin da suka samu daga wannan irin shuka da suka jarraba a kasa da watanni biyu kacal’’.

Farfesan ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da jihohi da kuma kananan hukumomi da su samar da hanyoyin da za su sa ayyukan noma su yi sauki. Hakan zai iya samar da riba mai yawa ga manoman.

Babu shakka harkar noma za ta ci gaba da samar da abin yi ga sama da kashi 66 na ‘yan Nijeriya, wanda hakan na nufin kimanin mutane miliyan 160 idan har aka ba shi kulawar da ta dace.

Farfesa Rabiu Adam jagoran binciken samar da irin masarar cewa ya yi, bayan kammala binciken kan irin mai jure wa nau’in cutar da ta addabi masarar, sun ba manoma zabi daga samfurin irin da aka inganta guda biyar da aka shuka su na gwaji, su ma su shuka domin ganin ingacinsu.

“Sai bayan sun shuka a matsayin gwaji sun kuma ga ingancin kowanne da gamsuwarsu ne za su fitar da zabinsu, mu kuma mika wa Gwamnatin Tarayya domin amince wa da shi”

Wannan ci-gaba ya samu yabo daga daya da ga cikin masu ruwa da tsaki a harkar, wato Shugaban kungiyar Manoman Masara reshen Jihar Kaduna, Kabir Salihu.

Shugaban ya jinjina tare da yaba wa cibiyar bisa wannan namijin kokari da ta yi na samar da nau’ikan irin shukawanda zai taimaka matuka wajen habaka noma da kuma wadatar da cimaka a kasa.

Ya ce ta irin haka ne aka samu ci-gba ta wannan fanni a lokacin da wata cuta ta addabi kubewa wanda aka yi ta fama a ‘yan shekarun baya na asarar da manoma suka yi ta tafkawa sakamakon cutar da ta addabi kubewar.

Cibiyar ta fara bincike a kan sabuwar cutar da ta kama gonakin kubewa a fadin kasar nan.

Kwararrun cibiyar suna gudanar da bincike a dakin gwaje-gwajen cibiyar domin gano ko wace irin cuta da kuma irin kwarin da ke yada ta.

An gano wannan cuta da take kama gonakin kubewa a sassan kasar nan, inda hakan ya jawo asarar sama da kashi 70 na kubewar.

Farfesa Ishaku ya ce, da cibiyar ta sami rahoton bullar cutar sai ta tura masana kimiyya zuwa sassan Jihar kaduna da wasu bangarorin domin gano halin da ake ciki.

A cewarsa, ‘‘cutar wata annoba ce domin ta yadu zuwa ko‘ina a kasar nan, kuma binciken gaggawa da masana kimiyyar cibiyar suka gudanar ya tabbatar da cewa kwayoyin cuta ce ke haifar da ita.

“Binciken masana ya nuna cewa, kwari ne ke yada wannan cuta, wanda kuma an gano babu maganin feshi da ke maganin ta’’ inj shi.

Babban Daraktar ya ce hanyar da ya kamata a bi kawai shi ne a yi amfani da maganin feshi domin magance kwarin da nufin magance yaduwar cutar.

Amma duk da haka, Farfesa Ishaku ya ce mutane za su iya yin amfani da ’ya’yan kubewar domin yin miya.

Ya shawarci manoma da su rika fesa wa gonakinsu magunguna kafin su yi shuka, kuma su rika samo iri a wuraren da suka dace.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja