An gano sassan mutum da aka binne a coci
Rundunar ’yan sandan Jihar Ogun ta gano sassan jikin mutum da aka binne a wani coci da ke unguwar Iyesi a Sango Ota. Kwamishinan ’yan sanda Ahmad Iliyasu, wanda ya jagoranci ’yan jarida zuwa cocin a shekaranjiya, ya shaida cewa bayanan sirri da rundunar ’yan sandan ta samu ne ta kai ga kame wani mutum […]
Rundunar ’yan sandan Jihar Ogun ta gano sassan jikin mutum da aka binne a wani coci da ke unguwar Iyesi a Sango Ota.
Kwamishinan ’yan sanda Ahmad Iliyasu, wanda ya jagoranci ’yan jarida zuwa cocin a shekaranjiya, ya shaida cewa bayanan sirri da rundunar ’yan sandan ta samu ne ta kai ga kame wani mutum mai suna Adeola, wanda ake zargi da ƙwarewa a harkar garkuwa da mutane; wanda shi ne ya ba bayyana cewa a cocin ne aka binne sassan jikin mutanen da ya yi garkuwar da su. “Bayan da ya nuna mana wani ɓangare a cikin cocin, da muka haƙe sai muka yi kiciɓis da abubuwan da muke kyautata zaton sassan jikin mutane ne. Don haka mun yi nisa cikin gudanar da bincike, za kuma mu tabbatar an hukunta duk wani mai hannu a ciki,” inji shi.
Sai dai Faston cocin mai suna Samuel Babatunde ya musanta zargin da aka yi masa, inda ya shaida cewa ba mutum ya binne ba, hasali dai ya binne alade da ransa ne a cocin domin nema wa mabiya cocin falala. A nasa ɓangaren Adeola wanda ake zargi da garkuwa da mutane, ya amsa laifinsa, ya kuma haƙiƙance cewa faston ya kai wa yara biyun da ya yi garkuwa da su a hanyar Iwo da ke Ibadan. Ya ce yaran mace da na miji ne kuma an ba shi Naira dubu 50 a kan kowane yaro.
A baya bayan nan dai jami’an tsaro na ci gaba da bankaɗo maɓoya da ake zargin matsafa da masu garkuwa da mutane na amfani da su a jihohin Legas da Ogun da Oyo da sauran jihohin Kudu maso yamma.