An gano shanun sata 44 a yankin Suleja

daya daga cikin fitattun mafarautan barayi a kasar nan, Alhaji Shehu Musa Aljan ya kora wani garken shanu a ranar Talata da ta gabata zuwa mahautar Suleja, wadanda ya ce shanun sata ne da ya samu nasarar gano su a kauyen Malam-Karu da ke kan hanyar Suleja zuwa Minna. Mafaraucin barayin wanda ya jagoranci tawagarsa […]

An gano shanun sata 44 a yankin Suleja
An gano shanun sata 44 a yankin Suleja

daya daga cikin fitattun mafarautan barayi a kasar nan, Alhaji Shehu Musa Aljan ya kora wani garken shanu a ranar Talata da ta gabata zuwa mahautar Suleja, wadanda ya ce shanun sata ne da ya samu nasarar gano su a kauyen Malam-Karu da ke kan hanyar Suleja zuwa Minna.
Mafaraucin barayin wanda ya jagoranci tawagarsa da ta kunshi yaransa da ’yan sanda, ya bayyana wa Aminiya jim kadan bayan isarsa mahautar cewa, sun samu nasarar gano shanun ne a wata ruga da ke kauyen, sakamakon bayanin da ya samu daga wajen wasu barayin shanu da ya kama, gabanin kai samamen. Haka nan ya ce ya samu nasarar kama wasu barayin bayan kama shanun, inda ya ce idan aka hada barayin da ya kama a farko adadinsu ya kai 12.
Da yake amsa tambaya a kan ko me ya sa ya zabi kai shanun zuwa mahautar maimakon wani waje daban da za a rika kiwata su kafin bayyanar masu su, Shehu Aljan ya ce a baya yakan kai dabbobin da ya kama ne zuwa wani babban ofishin ’yan sanda amma sai ya sauya shawara a wannan karo kasancewar kwatar na da yalwar fili, sannan kuma ba ta da nisa da daji inda za a rika kai shanun kiwo kafin bayyanar masu su.
Shanun wadanda adadinsu ya kai 44 ya ce an sato su ne daga jihohin Kaduna da Neja da Kogi da Nasarawa da kuma Zamfara.  Ya ce barayin kora shanun ne da taimakon wasu yaran Fulani da aka gano shanun a hanunsu. Yunkurin jin ta bakin daya daga cikin wadanda suka kaman, wanda kuma ke zaune a cikin daya daga cikin motocin ’yan sanda bai samu nasara ba, inda Shehu Aljan ya ce gabatar da shi na iya kawo cikas ga binciken da suke yi, ko kuma ya ba da damar gudun abokan tafiyarsu da ba su shiga hannu ba.    
daya daga cikin yara makiyaya uku da suka taimaka wajen kora shanun zuwa wajen, mai suna Magaji Sani ya ce jami’an tsaro karkashin jagorancin Shehu Aljan sun kai farmaki a rugarsu a jijjibin safiyar ranar a lokacin da suke tatsar nono daga shanun, daga nan ne kuma inji shi suka umarce su da su kora shanun zuwa wannan waje. Yaron ya ce ba a kama iyayensu ba, suna can ruga.
Sarkin Zangon Mahautar Suleja, Alhaji Magaji Namama ya ce za su ci gaba da kula da shanun har zuwa lokacin da masu suka bayyana.