An gano takun sawun mutane da ya shekara dubu 120 a Saudiyya
Ya nuna cewa, jama’a na ziyartar yankin tafkin don neman ruwa yayin da dabbobi ke zuwa yankin yin kiwo.
An gano wasu takun sawun mutane da na giwaye da wasu dabbobi a wani yankin tafki da ya bushe a kasar Saudiyya da ake jin an yi su ne shekara dubu 120 da suka shude.
An dai gano jerin takun sawun mutum bakwai a wani tafkin da ya bushe a Arewacin yankin Tabuka wanda ke nuna asalin Larabawa wadanda suka kasance mazauna a yankunan Arewa maso Gabas a Nahiyar Afirka.
- Matashi ya kai karar mahaifiyarsa kan korarsa daga gidanta
- Kotu ta yanke wa Donald Trump da Sarki Salman hukuncin kisa
Masana sun gano cewa, sawun akalla na mutum biyu ne, sannan suka ce hakan zai taimaka wajen yin binciken asalin mutanen da suka fito daga yankunan Nahiyar Afirka zuwa kasar Saudiyya.
A wani sabon bincike an wallafa cewa, “Asalin inda jama’ar suka fito ya biyo bayan tafki da kogunan da suke yankin, wanda hakan ya nuna muhimmancin jama’ar da suke yankin a cewar Mathew Stewart daga Cibiyar Chemical Ecology.
Mathew Stewart ya kara da cewa, “Ana iya gano takun sawun mutum musamman wadanda za a iya yin bincike a kai sakamakon yadda za a iya yin gwaji a kansa na wani lokaci ta hanyar daukar hotonsa, a iya gano adadin dadewarsa da kwanakin da ya yi, ba tare da an kiyasta adadin dadewarsa ta hanyar adana shi ba ko a rubuce.”
Binciken masu nazari ya nuna cewa, takun sawun na da kamanni da mutanen wannan zamani sakamakon yanayinsa da kuma na siffar jinsin mutanen da suka yi zamani a shekara dubu 40 da suka wuce wadanda a yanzu ba a san sun yi rayuwa a wannan yanki ba sai ta wannan dalili.
Mathew ya ce: “Mun san cewa dai jama’a na ziyartar tafkin yankin haka kuma akwai dabbobin da suke zuwa wuraren, sai dai ba a samu irin duwatsun da mutanen wannan lokacin ke amfani da su ba.
“Wannan na nuna cewa, jama’a na ziyartar yankin tafkin don neman ruwa yayin da dabbobi ke zuwa yankin yin kiwo,” inji shi.
Akalla takun sawun halittu 233 aka gano ciki har da na giwaye da wasu dabbobi.
A yau yankin Arewa maso Gabas a Nahiyar Afirka na da tarin sahara wanda jama’ar asalin yankin suka yi rayuwa sannan suka yi farautar dabbobi.
Binciken masana na nuna cewa, karni goma baya wasu yankunan na da kasar da take fitar da tsirrai da kuma danshi, amma kuma an samu sauyin yanayin da a yanzu yankin ya sauya.
Richard Clark-Wilson daga Jami’ar Royal Holloway, a birnin Landan, ya ce: “Wani lokaci da ya shude sahara ta mamaye yankin Arewa maso Gabashin Nahiyar Afirka daga bisani, bayan da aka samu sauyin yanayi aka rasa ciyawa da ruwa a tafkuna da kogunan yankin.”
“Samun wadatar dabbobi kamar giwaye da dorinar ruwa, na da nasaba ne da tsirrai da kuma wadatar albarkatun ruwa da ya hada da yankunan Arewacin Larabawa, wanda hakan ya fara bai wa jama’a damar tafiya a tsakanin Nahiyar Afirka da Nahiyar Turai, kamar yadda Michael Petraglia, daga Cibiyar Kimiyyar Tarihin Dan Adam ta Mad Planck ya yi karin haske.