An gano tsinkaye maƙale a ƙoƙon kan wani mutum a Vietnam

Ya sha fama da matsanancin ciwon kai har ma ya kai ga rasa gani a cikin watanni biyar.

An gano tsinkaye maƙale a ƙoƙon kan wani mutum a Vietnam

Hoton tsinkayen da aka gano a cikin kokon mutumin kasar Vietnam

Wani dan kasar Vietnam wanda ya sha fama da matsanancin ciwon kai har ma ya kai ga rasa gani a cikin watanni biyar da suka wuce, ya gano cewa, akwai tsinkayen cin abinci da suka makale a cikin kokon kansa.

An kwantar da mutumin da ba a bayyana sunansa ba kwanan nan a asibitin Cuba Friendship da ke birnin Dong Hoi, lardin Kuang Binh na kasar Vietnam, bayan ya yi korafin ciwon kai a-kai-a-kai da rashin gani da fitar ruwa daga hancinsa.

Lokacin da aka tambaye shi, mutumin ya bayyana cewa babu wani dalilin da zai iya haifar da wadannan alamomin, amma hoto ya nuna fargabar kamuwa da cutar da za a iya yi masa tiyata a kansa, wanda yake daidai da kamar tiyatar da ake yi bayan taruwar iska a cikin huhu da kuma wasu abubuwa biyu bakake da suka fito daga hancinsa zuwa cikin kwakwalwarsa.

Bayan an yi cikakken bincike, an gano abubuwan a matsayin tsinkayen cin abincin… Da aka tambaye shi ta yaya tsinken cin abincin ya shiga cikin kokon kansa, majinyacin mai shekara 35 da farko ya yi mamaki kamar yadda likitocinsa suka yi, amma daga bisani ya tuna wani al’amari da ya faru watanni biyar kafin hakan, wanda zai iya taimaka masa ya bayyana halin da yake ciki.

Yayin da yake fita shan giya da daddare, mutumin ya sami rashin lafiya kuma an kai shi dakin kulawar gaggawa.

Duk da haka, likitocin da ke wurin sun yi masa rigakafi kawai suka sallame shi daga sashen.

Yanzu yana dauka cewa dayan tsinken ya makale a cikin kwanyarsa, ta hanyar hancinsa, amma bai tuna ainihin abin da ya faru ba.

Ayarin likitocin sun yanke shawarar yin aikin tiyata na endoscopic ta hanci, tare da yi masa tiyata don rufe jijiyoyin da suke hade da kwakwalwarsa da kuma cire tsinkayen.

A cewar Nguyen Ban Man, Shugaban Sashen Kula da Fidar Kwakwalwa a asibitin Cuba Friendship Hospital, zabar mafi kyawun hanyar tiyata yana da mahimmanci don guje wa barin majiyyaci cikin yanayin yake fama da shi.

Yanayin mutumin mai shekara 35 ya daidaita kuma an sallame shi daga asibiti. Samun tsinkayan a cikin kokon kansa abun mamaki ne.

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele

Fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci N125m a 2025