An gano tsohon gari a karkashin birnin Jedda ta Saudiyya

Wasu masana dadaddun abubuwan duniya, sun gano burbushin wani birni da ke binne a karkashin tsohon birnin Jedda ta kasar Saudiyya, inda suka bayyana cewa, ‘a kansa aka gina gari na zamani.’ Masu binciken, sun gano tsohon birnin ne a lokacin da suke haka a wasu wurare na tsohon birnin. Majiya ta bayyana wa jaridar […]

An gano tsohon gari a karkashin birnin Jedda ta Saudiyya
An gano tsohon gari a karkashin birnin Jedda ta Saudiyya

Wasu masana dadaddun abubuwan duniya, sun gano burbushin wani birni da ke binne a karkashin tsohon birnin Jedda ta kasar Saudiyya, inda suka bayyana cewa, ‘a kansa aka gina gari na zamani.’

Masu binciken, sun gano tsohon birnin ne a lokacin da suke haka a wasu wurare na tsohon birnin. Majiya ta bayyana wa jaridar Ashark Al-Awsat, cewa ana neman izinin masu gidaje a wurin da aka tono birnin, don su bayar da dama a ci gaba da haka. Wannan yanki da aka gano burbushin gidajen tsohon birnin, yana kusa da Ain faraj.
Wata majiya ta ce: Akwai dimbin tarihi a tattare da wannan tsohon birni da muke zaune, don haka aka tabbatar akwai wani birni a cikinsa.”
Shi kuwa Sami Nawar, shugaban sashen yawan bude ido da al’adu na Jedda, ya bayyana wa Ashark Al-Awsat: “An binciko dimbin abubuwan da suka tabbatar da wannnan ikrarin. Misali mazaunan unguwar Al Mazloom yana ginin hanyar ruwa, mai zurfin mita shida, sai ya gano injinunan markade guda uku, tare da wasu kayayyakin.” A cewarsa, akwai dimbin abubuwan da aka gano a wannan yankin da dadewa.
Wani masanin tarihin tsohon birnin na Jedda, Abdul Wahab Abu Zanada, ya bayar da labara makamancin na Sami, inda ya bayyana cewa a ginin Malika da ke yankin Al Balad, ya gano daurin bama-bamai, wadanda ba su fashe ba, tare da wasu kayan tarihi.
“Zamanin da aka kai farmaki a kan birnin Siraf da ke daular Farisa, wasu daga cikin mazaunan birnin sun yi gudun hijira zuwa Jedda, ind asuka zauna, suka shinge birnin da ganuwar duwatsu, sannan suka haka makwararar ruwa. A shekarar 568, sun gina tankin ruwa mai zurfin mita hudu. Sai dai a yanzu ba na tunanin akwai burbushinsa,” inji shi.
Ahmad Bin dawood Al-Dinouri, a cikin littafinsa Al-Akhbar Al-Tuwail, ya ce, Sarki Iskandar ya shigo cikin Makka, a zamanin mulkin Al-Nidr Bin Kanan, sannan ya tsallaka teku daga Jedda zuwa kasar Moroko.
“Iskandar ya mutu a karni na hudu kafin haihuwar Annabi Isa (A.S.), wannan kuwa ke tabbatar da cewa akwai birnin Jedda tun a wancan zamanin,” domin a cewarsa: “kabilun kuda, wadanda suka rayu a karni na biyu kafin haihuwar Annabi Isa (A.S.) sun zauna a Jedda, al’amarin da ke nuni da cewa akwai wnanan birni tsawon zamani.”
Wani amsanin Umdah abdulSamad Mohammad abdulSamad, ya ce Jedda na da kima a tarihin Musulunci, domin Kalifa Usman dan Affana ya mayar da birnin tashar jirgin ruwa, don shiga birnin Makkah, tun a shekarar 647. Kuma Ibn Batoutah da Ibn Jubair duk sun yi bayani kan Jedda a rubuce-rubucensu. Masanin ya ce, Al-Ashraf kansuh Al-Ghawri, wanda ya taba mulkar birnin, shi ne sarki na karshe a jerin sarakunan daular Burji, wadanda suka gina wa birnin ganuwa, da kariya daga masu kawo hari.
Kuma a shekara ta 1050, wani matafiyi, Musulmin Farisa, Nassir Khusro, ya bayyana yadda ya ga birnin Jedda, cike da dogwayen gine-ginen da ke yi wa mutane maraba.