An gano uwar jaririn da ya makale a bututun kashi a kasar Sin

Wata mata ’yar shekara 22 da ta yi kururuwar jariri ya makale a bututun da kashi ke kwarara a kasar Sin, an gano ita ce uwar jaririn, inda ta boye kanta, tana kallo har ka shafe sa’o’i biyu ana kokarin cetonsa.Matar wadda kafafen yada labarai ba su bayyana sunanta ba, rahotanni sun tabbatar da cewa […]

An gano uwar jaririn da ya makale a bututun kashi a kasar Sin
An gano uwar jaririn da ya makale a bututun kashi a kasar Sin

Wata mata ’yar shekara 22 da ta yi kururuwar jariri ya makale a bututun da kashi ke kwarara a kasar Sin, an gano ita ce uwar jaririn, inda ta boye kanta, tana kallo har ka shafe sa’o’i biyu ana kokarin cetonsa.
Matar wadda kafafen yada labarai ba su bayyana sunanta ba, rahotanni sun tabbatar da cewa ta yi wa ’yan sanda ikrarin ita ce uwar jariri, amma duk da haka sun bukaci ta je a duba lafiyarta. Da aka gudanar da bincike a gidan da take haya, an samu kayan wasan yara da jini a jikin mayanin takarda katse kashi, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Zhejiang ya bayyana a shafin yanar sadarwarsa ya baza.
An kira jami’an kashe gobara, suka kutsa kai cikin ginin Pujiang da ke gabashin gundumar Zhejiang a birnin Jinhua, inda suka yi ta fafutikar ceton jariri da ya makale a wata kusurwa ta bututun kashi, da ke kasan wani makewayin al’umma da dakin hutu da ke jikin ginin.
Hoton bidiyon fafutikar ceton jaririn, wanda aka yi wa lakabi da Lamba 59 “No. 59” saboda lambar jaririn ke nan a lokacin da yake kwance a cikin gilashin dumama jarirai a asibiti, an nuna shi a kafafen yada labaran China da shafukan sadarwar intanet, a ranar Litinin din da ta gabata. Labarin wannan jariri ya bazu ko’ina a duniya, saboda tashin hankalin da ya shiga aka yi ta aiko masa da taimako.

An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda