An gargaɗi ’yan acaɓa kan ɗaukar fasinjoji 2 da daddare a Gombe

Ina so wannan matsala ta kwacen babura ta zama tarihi saboda na samu abin da zan yi alfahari a nan gaba.

An gargaɗi ’yan acaɓa kan ɗaukar fasinjoji 2 da daddare a Gombe

Masu sana’ar acaba

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Gombe, CP Hayatu Usman, ya gargadi ’yan acaban da ke watsi da shawarwarin da ake ba su na kaucewa daukar fasinja biyu ko uku suna shiga lungu da daddare, inda galibi a sanadiyar haka suke fada wa tarkon masu kwacen babura.

Kwamishina Hayatu ya yi gargadin ne a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a ofishinsa, yana mai cewa an fi samu ta’adar kwacen baburan ’yan acaba da daddare musamman ga masu daukar fasinja fiye da daya.

Ya ce “an ja musu kunne, an musu gargadi kan haka domin kauwace shiga tarkon bata-garin amma ba su daukar shawara.

Ya bayyana cewa galibi wannan matsalar tana faruwa ne a bayan gari a yankin Akko da ke daura da unguwannin Wuro biriji da Gona.

A cewarsa, zai yi zama na musamman da mutanen unguwannin kamar yadda suka nema domin samar da mafita.

CP Hayatu Usman ya ce zai ja hankalin al’ummar yankin domin a hada karfi da karfe don ganin an shawo kan matsalar kwacen babura.

Ya bayyana fatansa na samun mafita da zarar an tattauna da mutanen unguwannin domin daukar kwararan matakai da za su magance matsalar baki daya.

Ya ci gaba da cewa, yana so wannan matsala ta kwacen babura ta zama tarihi saboda ya samu abin da zai yi alfahari a nan gaba.

Ya ce duk da kasancewarsa sabon Kwamishina ’yan sandan Jihar Gombe, yana da masaniyar yadda al’amura ke gudana saboda kafin yanzu shi ne Mukaddashin Kwamishina ’Yan sanda mai kula da bangaren ayyuka ’yan sanda.

A cewarsa, yana da gogewar da zai kawo kyakkyawan shiri kan samar wa matasa mafita a rayuwa wajen samar musu sana’oin hannu wasu kuma a mayar da su makaranta domin da yawa suna zama bata gari ne saboda rashin aikin yi wanda a doka hakan ba hujja ba ne.

Ya yi kira ga sauran jami’an tsaro da su bai wa ’yan sanda hadin kai wajen ganin sun hadu sun gudanar da aikin su gaba daya.

Kazalika, ya jinjina wa ’yan banga da mafarauta da suke aiki tare da jami’an tsaro ba dare ba rana wajen shiga daji domin dakile aika-aikar ’yan ta’adda da barayi da masu satar mutane domin karbar kudin fansa.

Haka kuma, ya ja kunnen jami’an ’yan sanda da su kiyaye sanya hannunsu a mummunar dabi’ar karbar cin hanci ko zaluntar al’umma a gari.

Ya ce duk jami’in da aka kama zai dandana kudarsa domin hakan ya zama izina saboda idan ba tare da hadin kan jama’a ba aikin su ba zai yi nasara ba.