An gargadi al’umma game da la’antar shugabanni
Rabaran Isaac Gbadero na Majami’ar Baptis da ke Sabon Garin Zariya a Jihar Kaduna ne ya yi kira ga jama’a da su koma ga Allah a maimakon dogaro da wasu don samun biyan bukatar rayuwa. Ya yi wannan kira ne a sakonsa na bikin Kirsimeti ga daukacin al’ummar Najeriya. Ya ce dukkan masifun da muke […]

Rabaran Isaac Gbadero na Majami’ar Baptis da ke Sabon Garin Zariya a Jihar Kaduna ne ya yi kira ga jama’a da su koma ga Allah a maimakon dogaro da wasu don samun biyan bukatar rayuwa.
Ya yi wannan kira ne a sakonsa na bikin Kirsimeti ga daukacin al’ummar Najeriya. Ya ce dukkan masifun da muke fuskanta sun samo asali ne bisa yadda ba mu sanya Allah a cikin lamurranmu.
Ya ce duk wanda yake karatun littafi mai tsarki zai ga hakan a wurare da yawa na ayoyi, wadanda suke nuna cewa a karshen zamani za a ga abubuwan tashin hankali da ban tsoro, kuma kauyawa za su dawo birane suna gine-gine masu tsada. “Haka yake a cikin addinin Musulunci, duk wanda yake karanta sakon Annabi Muhammadu (S.A.W) zai ga haka,” inji shi.
Rabaran Gbadero ya kuma gargadi masu zagin shuwagabanni da su daina, domin ba shi da amfani kuma ya nemi al’ummada a kullum su rika yi masu addu’o’i da fatan alheri ga shugabanni da kasa, don ingantuwar rayuwarmu.
Da ya juya kan masu garkuwa da mutane kuwa, Rabaran ya bukace su da su ji tsaoron Allah, su daina kuma su tuba zuwa ga Ubangiji don samun tsira daga mai ceto.