An gargadi Fulani a Kurmi su kula da ’ya’yansu
A ci gaba da kokarin shuwagabannin Filani a Kudu maso yamma ke yi domin inganta tsaro da kyautata alakarsu da Yarabawan yankin, Shugaban kungiyar Miyyati Allah reshen Jihar Ekiti, Alhaji Muhammadu Nasamu ya kira taron shuwagabanni da daukacin dattawan Fulanin yankin domin lalubo bakin zaren matsalolin da ake alakanta su da ita. Shugaban ya shaida […]
A ci gaba da kokarin shuwagabannin Filani a Kudu maso yamma ke yi domin inganta tsaro da kyautata alakarsu da Yarabawan yankin, Shugaban kungiyar Miyyati Allah reshen Jihar Ekiti, Alhaji Muhammadu Nasamu ya kira taron shuwagabanni da daukacin dattawan Fulanin yankin domin lalubo bakin zaren matsalolin da ake alakanta su da ita.
Shugaban ya shaida wa Aminiya cewa ya kira taron ne domin irin bakin jinin da aka shafa masu, don haka ya zama wajibi a kansu da su nemi hanyar wanke kansu. “In akwai wadanda suka san akwai bata gari a cikinsu, su fada, in babu su fada mana don mun san abin da za mu yi. In kana ganin danka da bakin abokai, ka gan shi da su yau, ka gan shi da su gobe; ya kamata ka kira shi, ka zaunar da shi, ka tambaye shi shin wadannan abokai baki daga ina suka zo kuma mece ce sana’arsu?” Inji shi.
Ya ce wannan na daga cikin dalilan da ya sa ya kira taron kuma duk sun ji sun gamsu da bayanan, yadda kowa zai je ya kula da yaronsa. Ya kara da cewa matsalar shaye-shaye da yawon banza da ’ya’yan Fulanin Jihar Ekiti ke yi duk suna so ya zama tarihi kuma suna daukar mataki.
Shi kuwa Sakateren kungiyar Miyyati Allah a Jihar Ekiti, Malam Zayyanu Muhammad kira ya yi ga hukuma da a rika yi musu adalci wajen daina alakanta su da satar mutane domin amsar kudin fansa. Ya nemi a hukunta wadanda aka kama da laifin tsare Olu Falae. “Tun da dai an yi nasarar kame masu laifin, sai a hukunta su kuma wadanda abin bai shafe su ba a sakar masu mara su ci gaba da harkokinsu kamar yadda aka saba, domin sun shafe shekaru aru-aru suna zaune lafiya da kabilun yankin kuma su ba su da hannu a garkuwar, kana sun yi tir da hakan.”
Ya kuma yi kira ga gwamnatocin da su kai masu dauki, domin magance irin tsangwamar da ake yi wa Fulani makiyaya tun bayan da kurar garkuwa da Cif Olu Falae ta taso.”