An gargadi jama’a su yi hattara da sayen tsohuwar wayar hannu
Sarkin Barebarin Jihar Ogun Alhaji Muhammadu Gana ya yi kira ga ’yan Arewa mazauna jihar su guji sayen wayar salula ta hannu da aka yi amfani da ita. Ya ce akasarin irin wadannan wayoyin hannu da jama’a kan saya na sata ne kuma hakan na jefa masu mu’amala da irin waɗannan wayoyin hannu cikin tsaka-mai-wuya. […]

Sarkin Barebarin Jihar Ogun Alhaji Muhammadu Gana ya yi kira ga ’yan Arewa mazauna jihar su guji sayen wayar salula ta hannu da aka yi amfani da ita. Ya ce akasarin irin wadannan wayoyin hannu da jama’a kan saya na sata ne kuma hakan na jefa masu mu’amala da irin waɗannan wayoyin hannu cikin tsaka-mai-wuya.
“Sau tari son banza ke sanya mutum ya sayi wayar hannu har ta jefa shi cikin matsala. A wannan lokaci ko nawa kake da shi za ka samu sabuwar waya a kwalinta tare da takardar shaida ta daidai kuɗinka. Don haka babu hujjar da zai sanya mutum ya sayi kwancen waya. Kuma ba a nan gizo ke saƙar ba, domin a yanzu an ci gaba. Duk wanda ya sayi wayar sata, jami’an tsaro za su iya binciko shi su kama shi, ya kuma fuskanci hukunci,” inji shi.
Mai Kanurin ya bayyana haka ne a yayin taron wayar wa jama’a kai da ya gudana a fadarsa da ke garin Shagamu a makon jiya. A cewarsa, ƙaurace wa sayen kwancen waya zai magance yawaitar satar wayar salula da a yanzu ya zama ruwan dare. Ya ce a makon jiya wani mutum ya sayi kwancen waya a hannun wata mata a garin Abeokuta, bayan wani lokaci jami’an tsaro suka gano shi ta hanyar binciken fasahar zamani, inda suka kama shi domin kuwa asalin wayar sato ta aka yi.
A ’yan kwanakin nan, an yi ta samun mutanen da ke shiga tsaka-mai-wuya bayan da suka sayi kwanecn wayar salula a Ogun, lamarin da ya sanya shugabannin yankin suka ga ya dace su wayar wa al’umma kai bisa illolin yin hakan.
A dayan ɓangaren kuma, Sarkin Barebarin yana cigiyar dangin wani direban mota ɗan ƙabilar Kanuri, wanda ’yan sanda suka tsinci gawarsa a ɗaure a kan babbar hanyar Legas daga Ibadan kusa da garin Ogere.
Ya ce, “’Yan sanda sun gano gawar bawan Allah hannunsa a ɗaɗɗaure ne sai suka kai wa Sarkin Hausawan Ogere Alhaji Abdullahi Saminaka sai ya sa aka wanke fuskarsa, nan aka gano yana da tsage irin namu na Barebari sai ya sa aka kawo shi nan fadata bayan mun ɗauki hotonsa, jama’armu suka haɗa kuɗi aka kai gawar ɗakin adana gawa daga nan muka yi cigiyar dangin mamacin har bayan kwana 7 ba mu samu wanda ya zo ba. Da na ga haka sai na nemi izini muka yi wa gawar sutura, jama’armu ta sallace ta aka binne ta, sai dai har yanzu muna da hoton mamacin. Kirana ga duk wani wanda ya rasa ɗan uwansa direba ɗan Kanuri a wannan tsakani, to ya zo da hotonsa fadarmu, domin a tantance a kuma sanar masa ibtila’in da ɗan uwan nasa ya haɗu da shi.” Ya ƙara da cewa ana samun wadansu ɓatagari da ke tsare direbobi su ɗaure su, su yi musu fashi a kan hanyar Legas daga Ibadan. Ya ce mutumin da ’yan sandan suka tsinto, ba ya dauke da wata alama da ke shaida sunansa ko garin da ya fito a tare da shi, face tsagen fuskarsa na Kanuri.