An gargadi manoma da su maido rancen kayan noma da aka ba su a Jigawa
Gwamnatin Jihar Jigawa ta bukaci manoman da aka bai wa rancen aikin gona su rika biyan rance da gwamnatin jihar ta ba su domin shirin ya amfani sauran manoma da gwamnatin ta ke da burin tallafawa a fadin jihar ta Jigawa. Jawabin hakan ya fito ne daga bakin mai bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin […]
Gwamnatin Jihar Jigawa ta bukaci manoman da aka bai wa rancen aikin gona su rika biyan rance da gwamnatin jihar ta ba su domin shirin ya amfani sauran manoma da gwamnatin ta ke da burin tallafawa a fadin jihar ta Jigawa.
Jawabin hakan ya fito ne daga bakin mai bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin kungiyoyi, Alhaji Muhammed Hamza Hadeja, a wani taron kungiyoyi da aka shirya a dakin taro na Three Star da ke Dutse a makon jiya.
Ya ci gaba da cewa a kokarin gwamnatin na bunkasa harkokin matasa da inganta aikin noma a jihar, gwamnatin ta kashe biliyoyin Naira wajen sayen kayan aikin noma na zamani wadanda aka raba wa manoman jihar kuma dubban manoma sun amfana da rancen.
Ya yi korafin cewa kayan aikin noman da gwamnatin ta saya ta raba wa manoman jihar tun a shekarar 2015 bisa alkawarin su biy a bai wa wadansu da suka ya hada da amalanke da shanun huda bayan shekara daya, amma da yawa daga cikinsu sun gaza biya.
Ya ci gaba da cewa kada fa su manta dukiyar gwamnati ba kayan banza ba ne, kuma dukiyar jama’ar Jihar Jigawa ce, yana mai cewa akwai bukatar su biya kayan domin wadansu ma su amfana, ya ce kayan gwamnati ne ba na wani ba ne, don haka su biya.
A karshe Mai bai wa Gwamnan Shawara ya bukaci jama’ar Jigawa su mara wa kyawawan manufofin Gwamna Badaru Abubakar na bunkasa aikin gona a jihar baya, a kokarinsa na samar wa matasa aikin yi da bunkasar tattalin arzikin jihar baki daya.