An gargadi ’yan Arewa masu zuwa ci-rani Kudu

Shugaban al’ummar Arewa mazauna Kudancin Najeriya a Jihar Edo, Alhaji Badamasi Saleh ya shawarci ’yan Arewa da suke kwarara zuwa Kudu da nufin ci-rani, da cewa su yi taka-tsan-tsan, domin guje wa fadawa cikin halaka, kamar yadda ta faru da wasu ’yan ci-ranin a kwanakin baya.Shugaban yana mai cewa: “Shawarar da zan ba masu zuwa […]

An gargadi ’yan Arewa masu zuwa ci-rani Kudu
An gargadi ’yan Arewa masu zuwa ci-rani Kudu

Shugaban al’ummar Arewa mazauna Kudancin Najeriya a Jihar Edo, Alhaji Badamasi Saleh ya shawarci ’yan Arewa da suke kwarara zuwa Kudu da nufin ci-rani, da cewa su yi taka-tsan-tsan, domin guje wa fadawa cikin halaka, kamar yadda ta faru da wasu ’yan ci-ranin a kwanakin baya.
Shugaban yana mai cewa: “Shawarar da zan ba masu zuwa ci-rani a nan Kudu, masu aikin kura-kura ko gadi ita ce, da farko su tabbatar shugabanni na kowane kwamiiti sun san da zuwansu. Wato su nemi sanin jagororin wurin, inda suka sauka da inda za a dauke su zuwa su yi leburanci. Sannan kuma su nuna wa shugabannin daga inda suka fito tare da rike lambobin wayoyin fitattun mutane daga garuruwansu na asali da kuma na nan Kudu, domin tabbatar da suna da gaskiya kuma su siffantu da halayya nakwarai.
“Amma idan har ya kasance suna yi wa wadannan jihohin shigar ganganci, to wannan zai kawo musu cikas sosai. Muddin shugabanin yankunan ba su san da zuwansu ba kuma ba su san su mutanen wane gari ba ne; sannan kuma har wa yau wadannan ’yan ci-rani su bar zuwa suna taruwa a wurin da ba a ba su izinin zama har su ce sun tare a waje, kamar gidansu na gado; maimakon irin haka ya kamata a ce sun hada kudi sun kama daki suna kwana a ciki, wanda haka zai kare musu mutuncinsu.”
Ya karkare da cewa: “A kullum mu shugabannin al’umma za mu dauki matakin ci gaba da kara wayar wa al’ummarmu kansu a kan muhimmancin rayuwa da zaman lafiya. Don haka su kuma masu daukar ’yan gadi, dole mu shugabanni ya zamana mun sani, domin ko da wani abu ya faru, za mu tsaya mu tabbatar mun bi musu kadinsu. Don haka duk wanda aka dauke shi zuwa yin gadi, za mu sa ido mu duba cancantar wurin. Saboda haka, muna shaida wa masu ba da gadi, su tabbatar ba su cusa ’yan uwa cikin wurin da ke da hadari ba.”