An garkame jaruma A’isha dan Kano a kurkuku

Babbar Kotun Majistare wacce ke zama a unguwar Nomansland a birnin Kano ta bayar da umarnin sakaya fitacciyar jarumar fina-finan Hausa mai suna A’isha Idris dan Kano a kurkuku bisa zargin aikata laifin bata suna da kuma zagin darakta Mu’azzam Idi Yari. dan sanda mai gabatar da kara Sajan Jacob Yaduma ya shaida wa kotu […]

An garkame jaruma A’isha dan Kano a kurkuku
An garkame jaruma A’isha dan Kano a kurkuku

Babbar Kotun Majistare wacce ke zama a unguwar Nomansland a birnin Kano ta bayar da umarnin sakaya fitacciyar jarumar fina-finan Hausa mai suna A’isha Idris dan Kano a kurkuku bisa zargin aikata laifin bata suna da kuma zagin darakta Mu’azzam Idi Yari.

dan sanda mai gabatar da kara Sajan Jacob Yaduma ya shaida wa kotu cewa darakta Mu’azzam Yari ne ya yi karar jarumar bisa laifin bata masa suna a wajen daukar wani fim a ranar 23 ga watan Satumbar da ya gabata.
“A wanann lokaci wacce ake zargin ta yi masa yarfen cewa yana watsewa da ’yan fim mata masu yawa, sannan ba don sana’ar fim da yake yi ba, to da haka zai kare rayuwarsa a matsayin mabaraci a bakin kasuwar ’yan kura.” Inji dan sandan.
Laifukan da ake zargin jarumar sun saba sashe na 392 da sashe na 399 na cikin kundin tsarin mulki na final kod.
Binciken Aminiya ya gano cewa cewa a lokacin da aka yi zaman kotun na farko a ranar 29 ga watan Satumba wacce ake zargin ta musanta laifukan da ake zargin ta da aikatawa, inda alkalin kotun Muktar dandago ya bayar da belinta a kan sharadin sanya hannu da ta yi za ta yi zaman lafiya tsakaninta da mai karar har na tsawon shekara biyu.
Sai dai a wannan zaman na biyu mai karar ya shaida wa kotu cewa jarumar da yake kara ta shiga har dakinsa a otel a yayin da suka ziyarci Jamhuriyyar Nijar a lokacin bikin sallar da ta gabata inda ta rika zazzaga masa ashariya.
Ya kuma shaida wa kotu cewa ya dauki muryar jarumar da wayarsa a lokacin da take zagin sa, inda ya nemi kotu ta amince masa ya bayyana shaidarsa, lamarin da alkali ya amince. A nan take kowa da yake kotun ya ji irin zagin da wacce ake zargi ta yi wa mai kara.
Alkalin ya janye batun belin da kotun ta bayar ga jarumar tun farko, saboda samun ta da keta alfarmar alkawarin da ta dauka tun farko, don haka ya bayar da umarnin sakaya ta a kurkuku. Sannan ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar 4 ga watan Nuwamba mai zuwa.