An garkame shi a gidan yari saboda koyar da musulunci a China
Hukumomin Kasar China sun garkame wani musulmi a gidan yari na tsawon shekara biyu sakamakon bude wani shafi a yanar gizon inda yake fadakar da jama’a al’amuran addinin muslunci tare da koya musu addinin. Wani shafin yanar gizo na hukumar kasar ya bayyana cewa an kama Huang Shike a shekarar 2016 a yankin Xinjiang watanni […]

Hukumomin Kasar China sun garkame wani musulmi a gidan yari na tsawon shekara biyu sakamakon bude wani shafi a yanar gizon inda yake fadakar da jama’a al’amuran addinin muslunci tare da koya musu addinin.
Wani shafin yanar gizo na hukumar kasar ya bayyana cewa an kama Huang Shike a shekarar 2016 a yankin Xinjiang watanni uku da suka gabata bayan da ya bude shafin koyar da addinin muslunci a kafar sada zumunta ta WeChat.
Hukumar ta c eta same shi da koyar da karatun Al’Kur’ani da sauran littattafan addinin musulunci a wani shafin sada zumunta na WeChat.
Hukumar ta ce fiye da mutum 100 ne suke bin Huang wanda daya ne daga cikin musulmin da ba su da rinjaye na kabilar Hui da ke kasar.