An garzaya da ’yan Isra’ila 154 asibiti bayan harin Iran

Ma’aikatar lafiyar Isra’ila ta ce wasu daga cikin majinyatan suna cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai

An garzaya da ’yan Isra’ila 154 asibiti bayan harin Iran

Isra’ila ta tabbatar cewa an garzaya da ’yan ƙasarta aƙalla 154 asibiti bayan sabbin hare-haren ramuwar gayya da Iran ta kawo mata.

Ma’aikatar lafiyar Isra’ila ta ce aƙalla mutum huɗu daga cikin waɗanda aka kai asibitin suna cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai, wasu biyar kuma na samun kulawa ta musamman saboda tsananin tashin hankali.

Alkaluman da ma’aikatar ta fitar sun nuna cewa mutum 130 daga cikin majinyatan sun samu raunuka marasa tsanani a sakamakon hare-haren.

Wannnan na zuwa ne a yayin da Iran ta ci gaba luguden rokoki a matsayin ramuwar gayya a sassan Isra’ila a a ranar Talata.

Isra’ila ta ce Iran ta lashe mata mutane akalla 24.

A ɗaya ɓangaren kuma Iran cewa harin tsokana da Isra’ila ta kai mata ya yi ajalin kimanin mutum 224.