An Gaza Samar Da Motocin Lantarki Bayan Watanni 10 Da Cire Tallafin Man Fetur

Babban ƙalubalen motoci masu amfani da lantarki shi ne samar da wutar da za a riƙa yi musu caji.

An Gaza Samar Da Motocin Lantarki Bayan Watanni 10 Da Cire Tallafin Man Fetur

Motoci masu amfani da Gas

Samar da motoci masu amfani da lantarki na ɗaya daga cikin alkawurran da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi wa ‘yan Najeriya bayan cire tallafin man fetur.

Sai dai gashi an kwashe watanni 10 ‘yan ƙasar na ɗanɗana kuɗarsu sakamakon rashin samar da motocin da aka yi alƙawari ga kuma litar mai ta doshi Naira ɗari bakwai.

Masu nazari a kan harkokin yau da kullum sun ce karsashi da nasarar ’yan Najeriya ta ragu ƙwarai da gaske a wuraren ayyuka, sakamakon tsadar sufuri da ya janyo matsananciyar wahalar rayuwa.

Kazalika, masu sana’o’in da suka ta’allaka a kan amfani da sufuri na ci gaba da kidaya asara.

Gwamnatin Tarayya ta yi aniyar ƙara yawan motocin da ke amfani da wutar lantarki a kasar nan zuwa kashi 7.50 na adadin waɗanda ake amfani da su zuwa baɗi.

Wannan aniya na nuna cewa aƙalla kaso 7.50 cikin motoci miliyan 11.8 da aka kiyasta a kan hanyoyin Najeriya a halin yanzu za su kasance masu amfani da wutar lantarki.

Sai dai wannan aiki na tafiyar hawainiya ƙwarai da gaske.

Mun tuntubi Jami’an Hukumar Kera Motoci ta Kasa NADDC kan halin da ake ciki dangane da aikin samar da motoci masu amfani wutar lantarki a kasar nan, amma haƙar mu bata cimma ruwa ba.

Gwamnoni na rige-rigen ƙaddamar da motocin lantarki

Gwamnonin Borno, Legas da Delta sun ɗan fara nuna sha’awarsu ga amfani da motoci masu amfani da lantarki.

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a bara ya ƙaddamar da motocin bas bas da kanana guda ɗari masu aiki da lantarki.

A wannan lokacin, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce, “Za mu kwaikwayi wannan hangen nesan naka da ka nuna, da kuma ƙwazo da ka bayyana a matakin jiha, domin kawo ci gaba ga jama’armu ta Najeriya baki ɗaya.

“Zulum kana yin abin da ya dace, aikin ka yana kyau ƙwarai da gaske, na gode sosai,”a cewar Tinubu

Shi ma dai Gwamnan Jihar Delta  Sheriff Oborevwori,  ya yunƙura kan wannan aiki na samar da motoci masu amfani da lantarki, inda ya kafa wani kwamiti na musamman kan aikin bayan ya ɗana waɗansu motoci masu amfani da lantarki da kamfanin Jet Motors suka harhaɗa a kwanakin baya.

Kazalika, a ranar 30 ga watan Afrilun 2023 ne Gwamnatin Jihar Lega ta sanar da ƙaddamar da  motocin bas masu amfani da wutar lantarki a karkashin shirinta na Legas Mass Transit Master Plan.

Akwai waɗansu jihohi da ke shirin fara irin wannan.

Akwai jan aiki a gaba — Masana

Masana sun bayyana cewa duk da yadda Gwamnati ke ganin cewa komawa amfani da motoci masu amfani da wutar lantarki sauƙi ne, akwai jan aiki idan an lura da yanayin wutar lantarkin da ake samarwa.

Wani injiniyan lantarki Ahmed Abdullahi, ya ce za a iya amfani da dokar samar da wutar lantarki ta jihohi su iya amfani da su don magance matsalar wutar lantarkin da ake samu domin tabbatar da aiki da motoci masu amfani da wuta.

“Dole a yi farin cikin shigo da motoci masu amfani da wutar lantarki, amma farin cikin zai iya zama na ɗan lokaci kaɗan ne.

“Ya kamata shugabanni su zuba jari mai yawa a fannin samar da wutar lantarki a birane da kauyuka.

“Saka hannun jari mai kauri a ɓangaren wutar lantarki ita ce hanya ɗaya da za a bi don tabbatar da yiwuwar amfani motocin lantarki ya.”

Abullahi ya ce akwai dubban mutane da har yanzu babu wutar lantarki a yankunansu.

“Don haka idan ana so a koma amfani da motoci masu amfani da wutar lantarki dole a samar da wuta.

Najeriya na da yawan al’umma sama da miliyan 220, kuma da kyar ake iya samar da wutar lantarki megawatt 5,000 ga gidaje da harkokin kasuwanci, duk da cewa tana da karfin samar da megawat 12,000 idan aka inganta dukkan tashoshin samar da wutar lantarki.

A halin yanzu dai Najeriya na iya samar da wutar lantarki daga megawatts 3,500 zuwa 4000, amma an ce sama da mutane miliyan 80 kwata-kwata ma ba su amfana da wutar lantarki a Najeriya.

Rashin wuraren caji a jihohi

Motoci masu amfani lantarki suna buƙatar a riƙa caja su  kai tsaye.

A yanzu jihohi kalilan ne ke da cibiyoyin caji, wanda waɗannan wuraren cajin su ne kan gaba wurin karɓuwa ko rashin karɓuwar motocin masu amfani da lantarki.

Hukumar kera motoci ta kasa (NADDC) a lokacin ƙaddamar da cibiyar cajin motocin lantarki mai amfani da hasken rana 15-KVA a jami’ar Nsukka ta Najeriya, a watan Agustan shekarar da ta gabata, ta ce ta samar da irin wannan cibiya a Jami’ar Legas da ta Usmanu Danfodiyo a Jihar Sakkwato.

An fara samun cibiyoyi masu zaman kansu a Legas, Cajin Hub a Abuja da Eride Nigeria a Maiduguri.

Wani kwararre a kan harkokin makamashi, Sesan Okunade, ya bayyana cewa, “sabuwar dokar samar da wutar lantarki da aka amince za ta taimaka wa jihohi wajen samar da wutar lantarki ta kashin kai.”

Ya kuma buƙaci gwamnatocin jihohi da su saka hannun jari a ayyukan more rayuwa da suka haɗa da cibiyoyin caji idan sun samu motocin lantarki.

Ya ce, “Ina ganin wani bangare na abubuwan da ya kamata jihohin Najeriya su yi, shi ne samar da ababen more rayuwa waɗanda ba shakka za su taimaka wajen tabbatar da cewa mutane sun samu wutar lantarki yadda ya kamata.”

Hakazalika, wani kwararre kan harkokin kasuwancin motoci, Dokta Oscar Odibo, a zantawarsa da Aminiya, ya buƙaci gwamnatocin jihohi da su sanya hannun jari a harkar hada-hadar motoci masu amfani da lantarki.

Wani tsohon mukaddashin Darakta-Janar na NADDC, Mamudu Lukman ya ce: “Babban ƙalubalen motoci masu amfani da lantarki shi ne samar da caji.”

Ya ce, “Bayanan da na tattaro na nuna cewa gwamnatocin jihohin da suka sayo wadannan motocin na yin caji ne daga wutar lantarki da ake tiro musu.

Haka lamarin yake a Borno, wanda kwanan nan aka ƙaddamar da motoci masu amfani da lantarki na haya guda 100.

Femi Owoeye, wani gogaggen dan jarida mai rubutu a kan harkokin motoci kuma mawallafin Kamfanin Motoring World International, ya shawarci jihohi da su saka hannun jari a fannin makamashi mai tsafta, musamman hasken rana, domin samar da wutar lantarki.

Ya ce, kowace jiha za ta iya kafa cibiyar caji mai amfani da hasken rana ta hanyar farawa da yankunan jihohin ko kuma babban birnin jihar kafin a  je ga kananan hukumomi.