An gina bene mai hawa 57 cikin kwana 19

Wani kamfanin gine-ginen kasar China mai suna Broad Sustainable Building ya wallafa wani faifan bidiyo wanda yake nuna yadda kamfanin ya gina wani bene mai hawa 57 bayan kwana 19 da fara aikin.  Benen da aka wa lakabi da sunan “Sky City” yana birnin Changsha ne , kuma ya kunshi gidaje guda 800 da ofisoshi […]

An gina bene mai hawa 57 cikin kwana 19
An gina bene mai hawa 57 cikin kwana 19

Wani kamfanin gine-ginen kasar China mai suna Broad Sustainable Building ya wallafa wani faifan bidiyo wanda yake nuna yadda kamfanin ya gina wani bene mai hawa 57 bayan kwana 19 da fara aikin. 

Benen da aka wa lakabi da sunan “Sky City” yana birnin Changsha ne , kuma ya kunshi gidaje guda 800 da ofisoshi da za su dauki ma’aikata akalla guda 4,000.
Da farko kamfanin ya yi shirin gina bene ne mai hawa 97 wanda zai zama ginin da ya fi kowanne tsawo a duniya. Amma saboda makwabtaka da wani filin jirgin da ginin ya yi, sai hukumomi suka bukaci da a rage tsawonsa zuwa hawa 57. Duk da tsaikon da aka samu, an kammala aikin ne gaba daya a kasa da makonni uku.
A faifan bidiyon mai tsawon mintuna hudu, an nuna leburori suna gina wasu bangarorin benen a wani wuri na daban, kafin daga bisani su dasa su bisa ginin. Daga karshe an nuna yadda aka kammala ginin, inda a kowace rana ake gina hawa uku na benen.

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogara da wani yanki ba – Ndume