An gina layin-dogo na karkashin kasa mafi tsawo a duniya

A shekaranjiya Laraba ne aka yi bikin bude wani layin-dogon karkashin kasa mafi tsawo a duniya a kasar Switzerland, bayan an shafe shekara 18 da fara gina shi.Layin-dogon na Gotthard Base, mai tsawon kilomita 57 (kimanin nisan tsakanin Birnin Kebbi zuwa Argungu), an gina shi a karkashin tsaunukan Alps, kuma an tsara shi ne da […]

An gina layin-dogo na karkashin kasa mafi tsawo a duniya
An gina layin-dogo na karkashin kasa mafi tsawo a duniya

A shekaranjiya Laraba ne aka yi bikin bude wani layin-dogon karkashin kasa mafi tsawo a duniya a kasar Switzerland, bayan an shafe shekara 18 da fara gina shi.
Layin-dogon na Gotthard Base, mai tsawon kilomita 57 (kimanin nisan tsakanin Birnin Kebbi zuwa Argungu), an gina shi a karkashin tsaunukan Alps, kuma an tsara shi ne da nufin rage cinkoson abin hawa a kan titunan Swiss, kamar yadda BBC ta bayyana.
Layin-dogon zai kasance daya daga cikin hanyoyin da ke danganawa da bangaren arewaci da kuma kudancin nahiyar Turai.
An bayyana hanyar jirgin kasar a matsayin mai kayatarwa, wanda aka kammala a kan kari, kuma a kan kudin da aka kasafta masa.
An ce aikin gina layin dogon ya ci Dala biliyan 12, kuma yayin aikin an fafe duwatsu, wadanda garin da aka rarake kadai zai kai a gina dalar dutse shida irin ta kasar Masar, don haka mahukuntan Switzerland sun ce aikin ya ci kudinsa.
A watan Disamba mai zuwa ne ake sa ran za a fara harkar kasuwanci ta layin-dogon, jiragen kaya sama da 250, da kuma jiragen fasinja 65 za su dinga yin jigila a kowace rana.