An girke jami’an tsaro a gidan Sheikh Abduljabbar
Gwamnatin ta girke jami’an tsaro gidan malamin don tabbatar da dokar da ta sa masa.
An girke jami’an tsaro a masallacin Sheikh Abduljabbar Sheikh Nasiru Kabara da ke unguwar Gwale, a Karamar Hukumar Gwale, Jihar Kano bayan ta rufe majalisinsa.
Aminiya ta gano akalla motocin jami’an tsaro biyar da aka girke a kofar gidan malamin, don tabbatar da bin umarnin da gwamnatin jihar ta kafa masa.
- Gwamnatin Kano ta rufe masallacin Sheikh Abduljabbar kan ‘batanci ga Sahabbai’
- Rufe masallaci: Sheikh Abduljabbar ya yi raddi
An girke jami’an tsaron ne, ’yan sa’o’i bayan Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar malamin daga yin wa’azi ko karatu a majalisinsa a fadin jihar, bayan zargin sa da batanci ga Sahabban Manzon Allah (S.A.W).
Gwamnatin ta kuma ba da umarnin dakatar da shi daga yin dukkanin wani abu da ya shafi addanin Musulunci a fadin Jihar, saboda gudun ta da zaune tsaye.
Sai dai Aminiya ta gano jami’an tsaron ba su hana mabiya da masu jaje ga malamin shiga gidan nasa ba.
Wakilinmu ya ga daruruwan almajiran malamin a wajen gidan da kofar masallacinsa na tururuwar yi masa jaje game da hukuncin da gwamnatin jihar ta dauka a kansa.
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, wanda mabiyin Darikar Kadiriyya ne, wasu malamai daga ciki da wajen jihar na ganin ya sauka daga layin koyarwar jamhurin Shugabannin Musulunci.