An gudanar da aikin raba katin zabe a Jihar Borno
Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta gudanar da aikin rarraba katin zabe na dindindin tare da sabunta rajista ga wadanda suka kai shekara 18 a kananan hukumomi 12 daga cikin 27 da ke Jihar Borno. Wadannan kannan hukumomi su ne suke karkashin ikon Gwamnatin Najeriya, yayin da sauran suka kasance a karkashin ikon kungiyar Boko […]
Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta gudanar da aikin rarraba katin zabe na dindindin tare da sabunta rajista ga wadanda suka kai shekara 18 a kananan hukumomi 12 daga cikin 27 da ke Jihar Borno.
Wadannan kannan hukumomi su ne suke karkashin ikon Gwamnatin Najeriya, yayin da sauran suka kasance a karkashin ikon kungiyar Boko Haram, kuma hukumar ta ce za ta yi iya kokarinta don yi wa ’yan gudun hijira da ke sansanoni da dama rajista don su samu su yi zabe.
Hukumar INEC ta fara aikin raba katin zaben ne a Maiduguri a ranar Asabar a akasarin rumfunan zabe suka fara gudanar da aikin rarraba katin zabe na dindindin ga jama’a.
Kuma a ranar Talata aka fara aikin yin rajista ga wadanda ba su da katin har zuwa jiya Alhamis.
Gwamnatin Jihar Borno ta ware ranar Talatar da ta gabata ta zama ranar hutu ga ma’aikata domin su fita su yanki katin zabe, kuma jama’a sun yi tururuwa zuwa rumfunan zabe domin karbar katin ko sake rajistar.
Mutane da dama da Aminiya ta tattauna da su sun nuna farin ciki kan karab katunan zabensu, inda suka ce hakan zai bas u damar zaben shugabannin da suke so.