An gudanar da bikin baje kolin kayan amfanin gona a Kano
Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin gudanar da taron Majalisar Harkokin Noma ta kasa a Jihar Kano badi. Ministan Gona Dokta Adeyemi Adeshina ya bayyana haka a wajen bikin baje kolin amfanin gona da aka yi a Bagauda da ke karamar Hukumar Bebeji ta Jihar Kano a karshen makon jiya. Ministan wanda Darakta a ma’aikatar, Mista […]
Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin gudanar da taron Majalisar Harkokin Noma ta kasa a Jihar Kano badi. Ministan Gona Dokta Adeyemi Adeshina ya bayyana haka a wajen bikin baje kolin amfanin gona da aka yi a Bagauda da ke karamar Hukumar Bebeji ta Jihar Kano a karshen makon jiya.
Ministan wanda Darakta a ma’aikatar, Mista Leo Imo ya wakilta, ya ce ma’aikatar ta yanke wannan shawara ce bisa la’akari da nasarorin da jihar ta samu wajen sauye-sauyen Gwamnatin Tarayya a bangaren noma.
A jawabi Gwamnan Jihar Kano wanda Mataimakinsa Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya wakilta ya ce bikin baje kolin amfanin gona biki ne da jihar ta shirya don manoma su baje ire-iren amfanin gonar da suke nomawa a jihar. “Baya ga ba manoma damar baje kolin kayan amfanin gonar da suke nomawa, har ila yau wannan biki zai taimaka wa manoman su hadu da cibiyoyin bincike kan ayyukan noma domin ci gabansu,” inji shi.
Kwamishinar Gona ta Jihar Kano Hajiya Baraka Sani ta ce bikin baje kolin zai bunkasa shirye-shiryen Gwamnatin Tarayya na wadata kasa da abinci. “Wannan biki zai ba manoma damar haduwa da juna tare da samun karin gogewa kan ayyukan noma. A gefe guda kuma bikin zai kara bunkasa shirin wadata kasa da abinci.”
Wasu daga cikin manoman da suka halarci bikin sun bayyana wa Aminiya farin cikinsu game da bikin, duk da cewa ba su samu ciniki sosai ba. Hajiya Fatima Muhammad ta ce “Mun kawo kayayyakin da muke nomawa kamar shinkafa da alkama da man-gyada kuma jama’a sun yaba kyawunsu. Duk da cewa ba mu samu ciniki sosai ba saboda rashin kudi a hannun mutane babu shakka mun ji dadin halartar bikin domin mun karu kan dabarun noma, mun kuma gana da kwararu a wannan bangare inda suka kare mu da shawarwari kan yadda za mu inganta ayyukanmu.”