An gudanar da kalankuwar raya al’adun gargajiya a Legas

A Litinin din da ta gabata ce aka kawo karshen bukukuwan nuna al’adun gargajiya na Jihar Legas, wanda aka gudanar a babban filin wasa na Tafawa balewa.Bikin, wanda aka yi masa lakabin ‘Lasgidi 2014.’ Ya samu halartar gungun matasa maza da mata da suka kware wajen rawar gargajiya da ta zamani daga kananan hukumomin jihar […]

An gudanar da kalankuwar raya al’adun gargajiya a Legas
An gudanar da kalankuwar raya al’adun gargajiya a Legas

A Litinin din da ta gabata ce aka kawo karshen bukukuwan nuna al’adun gargajiya na Jihar Legas, wanda aka gudanar a babban filin wasa na Tafawa balewa.
Bikin, wanda aka yi masa lakabin ‘Lasgidi 2014.’ Ya samu halartar gungun matasa maza da mata da suka kware wajen rawar gargajiya da ta zamani daga kananan hukumomin jihar daban-daban.
Sannan mayan baki daga ciki da wajen Najeriya tare da Gwamna Babatunde Raji Fashola da Ministan Ma’aikatar Shakatawa Da Yawon Bude Idanu da sarakunan gargajiya sun kashe kwarkwatar idonsu, haka zalika  makada da mawaka iri-iri sun nuna bajintarsu a mako guda da aka yi ana bikin a sassa da dama na jihar.
An gudanar da wasanni daban-daban da suka hada da tseren tukin jirgin ruwa da wasannin motsa jiki da wasannin nuna gwaninta don debe wa bakin da suka halarci bikin kewa.
Da yake jawabi Gwamnan Jihar Legas, Babatunde Raji Fashola ya bukaci mazauna jihar su rika sanya ido tare da zama lafiya tsakanin su da juna don samun bunkasar tattalin arziki a jihar.
Ya ce: “Ba yadda za a samu ci gaba da bunkasar tattalin arziki sai da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Idan babu zaman lafiya da kwanciyar hankali babu yadda jama’a za su ci gaba. Hakan ita ce kadai hanyar da za ta bunkasa harkar shakatawa da yawon bude ido a kasar nan.”
A nasa jawabin, Ministan Harkokin Yawon Bude Ido Da Shakatawa, Mista Edem Duke, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a harkar bikin su ba al’adun gargajiya muhimmanci don bunkasar bikin a kasa baki daya.